Liverpool ta karbi bakuncin Villarreal a Gasar Zakarun Turai, inda ta ragargaje ta da ci 2 babu ko daya.
Liverpool ta yi kane-kane tun a mintin farko na wasan, inda ta dinga yi wa Villarreal ruwan hare-hare.
- Yadda jama’a suka tashi lakada wa dan majalisarsu duka
- DAGA LARABA: Yadda Za A Magance Matsalar Tsaro A Arewacin Najeriya —Masana
An shafe kashin farko na wasan ba tare da an zura wa kowace kungiya kwallo a raga ba, har aka tafi hutun rabin lokaci babu ci.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci dan wasan bayan Villarreal, Estupinan ya yi rashin sa’a wajen zura kwallo a ragar kungiyarsa a minti na 53.
A minti na 55 ne dan wasan gaban Liverpool Sadio Mane ya sake zura mata kwallo.
Liverpool ta kai hare-hare har guda 20 a wasan, inda guda 15 daga ciki suka yi fadi, sai guda biyar da suka zama masu hatsari.
Ita kuwa Villarreal hari daya ta kai kacal, kuma shi ma ya yi fadi.