✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Liverpool ta sayi Darwin Nunez a kan Yuro 75m

Darwin Nunez ya zama dan wasa mafi tsada a tarihin Liverpool

Kungiyar kwallon kafa ta Benfica ta sanar da sallama dan wasanta, Darwin Nunez, ga Liverpool kan kudin Yuro miliyan 75.

Benfica ta sanar da kammala yarjejeniyar cinikayya tsakaninta da Liverpool da ke Ingila, kan dan wasan gaban nata ne a ranar Litinin.

Kazalika, Liverpool za ta bai wa Nunez alawus din Yuro miliyan 25 na sanya hannu da ya mata da kuma karin wasu kudin, wanda zai sa kudin da aka saye shi ya kai Yuro miliyan 100.

Ana sa ran Nunez zai shiga sahun ’yan wasan gaban Liverpool irin su  Mohamed Salahda Luis Diaz da Diogo Jota da kuma Roberto Firmino, a daidai lokacin da ake harsashen Sadio Mane zai bar kungiyar zuwa Bayern Munich.

Dan wasan dan asalin kasar Uruguay ya zama dan wasa mafi tsada da Liverpool ta taba siya, baya ga dan wasan bayanta Virgil dan Dijk daga Southampton kan Yuro miliyan 85.

A kakar wasan da ta gabata, Darwin Nunez, ya zura wa kungiyar kwallo 34 daga wasanni 41 da ya buga.