✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Liverpool ta lallasa Man City da ci 3 da nema

Rafari ya busa. Liverpool ta lallasa Man City da ci uku da nema. Salah ne ya fara zura kwallo, sai Chamberlain ya zura na biyu…

Rafari ya busa. Liverpool ta lallasa Man City da ci uku da nema. Salah ne ya fara zura kwallo, sai Chamberlain ya zura na biyu din, sannan kuma Salah ya taimakawa Mane shi me ya zura na ukun. Man City ba su samu damar gwada mai tsaron gidan Liverpool ba yada ya kamata duk da cewa sun kai har sau biyar, amma dukansu babu wanda ya yi kusa da shiga raga.

Kididdiga dai ya nuna cewa Man City sun fi taka leda a wasan, domin sun juya leda (pass) guda 738 Liverpool kuma guda 378.

Sai kuma karo biyu inda za a je gidan Man City, inda za su nemi akalla kwallo hudu.

An kara minti 3. Ko wani abu na iya faruwa a wannan mitnti ukun?

85; Kyaftin din Liverpool Henderson ya samu katin gargadi, amma kuma kash! ba zai buga wasa mai zuwa ba

84: Goallll…………….. Man City ta zura kwallo, amma rafari ha busa satar gida. Har yanzu Liverpool 3 Man City 0

82 Mane ya samu dama mai kyau, amma yi da kyau ba.

Ynzu dai kusan duk ‘yan wasan Liverpool sun tare a gida da nufin hana Man City zura musu kwallo

Saura minti 10 kacal. Ko Man City za ta yi wani abu kuwa?

Minti 73: Har yanzu dai Man City suna kokarin farkewa, amma Liverpool suna ta kokarin hana su.

An tafi hutun rabin lokaci yanzu.Liverpool 3 Man City 0. Salah da Chamberlain da Mane ne suka zura kwallaye. Ko Man City za su farke ko kuma Liverpool za su kara musu. Sai an dawo tukunan za mu gani

An kara minti biyu kafin hutun rabin lokaci. Har yanzu dai Liverpool 3  Man City 0

45: Fernadinho na gwada sa’a daga nesa, amma kwallon ta bude da yawa.

43: Saura kiris Man City ta zura kwallo bayan Komapany ya bugo bugun tzara amma kwallon ta yi sama da yawa

Minti 40: Har yanzu ana ci gaba da taka leda, kuma har yanzu dai Liverpool ke kokarin kara zura kwallo

Yau ne za goge raini tsakanin Liverpool da  Manchester City a wasan zagaye na farko na zakarun Turai. Yanzu haka an buga minti 34 kuma Liverpool na doke Manchester City da ci 3 da nema.