Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta je har gidan Inter Milan ta doke ta da ci biyu a gaban magoya bayanta a Gasar Zakarun Turai.
Wasan da kungiyoyin biyu suka buga a matakin ’yan 16, an yi dauki-ba-dadi kafin daga bisani Liverpool ta samu nasarar jefa kwallaye biyu.
- NAJERIYA A YAU: Wahalar Man Fetur: ’Yan Abuja Na Yaba Wa Aya Zakinta
- Babu jami’in da za mu yi wa rufa-rufa a badakalar hodar Iblis —NDLEA
An shafe kashin farko ma wasan ba tare da kowa ya zura kwallo a ragar abokiyar hammayarsa ba; Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Liverpool ta fara zura kwallo ta farko.
Dan wasan gaban Liverpool, Robert Firmino, ne ya fara jefa kwallo a minti na 75, kafin daga bisani Mohamed Salah ya jefa ta biyu a minti na 83.
Yanzu haka dai kafar Inter Milan daya na waje daya kuma na cikin gasar, har zuwa lokacin da za su sake karawa a karo na biyu a filin wasan Liverpool, wato Anfield.