✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Littafin Amina: kirkirarren labarin da ya tattaro matsalolin al’ummar Najeriya

Sunan Littafi: Amina.Sunan Marubuci: Mohammed Umar.Kamfanin Wallafa: ABU Press Limited, Zaria.Shekarar Wallafa: 2009.Yawan Shafi: Babi 27, Shafuka 371.Farashi: Ba a fada ba. Littafin ‘Amina’ kirkirarren…

Sunan Littafi: Amina.
Sunan Marubuci: Mohammed Umar.
Kamfanin Wallafa: ABU Press Limited, Zaria.
Shekarar Wallafa: 2009.
Yawan Shafi: Babi 27, Shafuka 371.
Farashi: Ba a fada ba.

Littafin ‘Amina’ kirkirarren labari ne da aka rubuta da ingantacciya kuma balagaggiyar Hausa. Yana ba da labarin wata matar aure ce, Amina, wadda ta zabi ta yi zaman aure na da’iman da mijinta, Alhaji Haruna, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Jihar Bakaro, duk kuwa da cewa ta yi karatun zamani mai zurfi (digiri).
Inda gizo ke sakar shi ne, inda muradinta da ra’ayinta na rayuwa suka bambanta da na mijinta da kuma na wasu kawayenta. A yayin da mijinta ya kasance dan siyasa mara tausayin talakawa, wanda ya kware wajen satar kudin gwamnati, kuma ya kware wajen kwangilar kashe-mu-raba kuma yake son matarsa ta kasance mai bin gurbataccen ra’ayinsa, ita kuwa Amina ta kasance mai tausayin al’umma, mai son a yi gaskiya tare da son tsare ka’idojin addinin Musulunci. Wadannan bambance-bambance da ke tsakaninta da mijinta, su suka haddasa rashin jituwa a tsakaninsu, ta yadda zamansu na aure ya yi ta gamuwa da matsaloli daban-daban.
Rayuwar Amina ta cika ta tumbatsa, ta shafi rukunnan al’ummomi daban-daban, ta yadda ta fito da matsalolin da suka yi wa al’umma cacukwi. Irin wadannan matsaloli sun hada da rashin tausayi irin na shugabanni, talaucin da ya yi wa al’umma kanta, cututtuka da suka addabi al’umma kuma ba tare da kulawar gwamnati ba. Haka kuma akwai matsalolin da suka shafi yadda kasashen Turawa suke taimakawa wajen durkusar da kasashen Afirika da sauransu. Irin yadda ake gwamutsa al’adun gargajiya da addini wajen tafiyar da rayuwar al’umma, ya fito fili a cikin wannan littafi, musamman ma abin da ya danganci zaman aure, mulki da sauransu.
Kamar yadda mawallafa littafin suka bayyana, an fassara shi zuwa yarukan duniya sama da ashirin, wadanda suka hada da Ingilishi da Girkanci da Sabiyanci da Larabci da Urdu, da sauransu. Haka kuma, akwai littafin cikin yarukan Chaina da Indonesiya da Koriya da Rasha da Punjabi da Kanada da Tamil da sauransu.
Idan mutum ya nazarci muhimman sakonnin da ke kunshe cikin littafin ‘Amina’ da kuma yadda aka tsaya tsayin daga aka rubuta shi cikin kyakkyawar Hausa, zai iya tabbatar da cewa littafin ya shiga cikin rukunin littattafai guda uku na Hausa, mafiya inganci a wannan zamanin. Wadannan littattafai kuwa su ne karshen Alewa kasa na Bature Gagare, ’Yartsana na Ibrahim Sheme da kuma Mace Mutum na Rahma Abdulmajid.
Wasu daga cikin sakonnin da littafin nan yake kunshe da su, sun hada da fadakarwa da wayar da kan al’umma, domin su san muhimmancin siyasa, ta yadda za su sanya ido ga yadda masu mulkinsu ke tafiyar da mulkinsu. Dubi abin da Fatima, wata mai fafutukar kare hakkin talakawa kuma kawa ga Amina take fahimtar da ita al’amarin siyasa: “Ko kin so, ko kin ki, kowane dan Adam dai dan siyasa ne. Abin ji dai kawai shi ne, ko dai ki shiga ciki a dama da ke, ko kuma ki hau kujerar ’yan-ba-ruwanmu. Idan kika yi watsi da yadda ake gudanar da harkokin rayuwarki, kina kallo wasu za su kama ragamar su yi yadda suke so da ke. A jujjuya ki kamar waina ba ki da ta cewa ko ba ki cewa uffan. Zabi ya rage gare ki.” Shafi na 16.
Wani darasi kuma da ya fito karara, shi ne na kira ga al’umma, musamman ma mata da su tashi su nemi ilimi. Mu dubi yadda Fatima ke zayyana fa’idar haka ga Amina, a shafi na 24 na littafin; inda take cewa: “Ni dai ga shawarar da zan ba ki: Ki kirawo matan da ke nan kusa da ke, ki nemi ilimantar da su abubuwan da suka shafe su. Ki bude masu idanu su gane ita duniyar da suke cikinta baro-baro. Wani ya taba cewa muddin mutum yana iya karatu, shi kam wannan ya sami cikakken ’yanci. Ki nuna masu yadda za su more rayuwarsu, cikin koshin lafiya da farin ciki.”
Labarin kuma yana jan hankali da tunasar da al’umma su koma ga koyarwar addinin Musulunci, musamman ma ta hanyar nazarin sakonnin da shi kansa Manzon Tsira (SAW) ya karantar. Babban misalin da marubucin nan ya kawo, shi ne na Hudubar karshe ta Manzon Allah mai tsira da aminci, wadda ya zayyana ta dalla-dalla a shafi na 74 zuwa 75 na littafin.
Akwai darasin da ke nuna muhimmancin kafa kungiya, musamman ma yadda Amina ta ba da misali, inda ta kafa kungiyar Matan Bakaro. Ta hanyar wannan kungiya suka samu hadin kai, suka san muhimmanci da tasirin kansu da muhimmancin da ke tattare da sana’a.
Haka kuma, akwai wani darasi mai muhimmanci, wanda ke nuna cewa duk wanda ya mike ya nema, zai iya samu, ko mace ko namiji. Dubi dai yadda ita kanta Amina ta samu nasara a fagen da ta dauka na tallafa wa mata da marasa galihu. Dubi kuma yadda Fatima ta yi fice kuma ta yi suna a fagen da ta dauka na gwagwarmaya da yaki da zalunci. Dubi kuma yadda Barista Rabi Usman ta gudanar da aikinta na lauya, duk da cewa mace ce, amma saboda kwarewa da jajircewa, ta kwato wa Amina da sauran matan Bakaro ’yancinsu; ta kwace su daga hannun zalunci.
Kamar yadda na fada a baya, littafin nan ya rubutu, haka kuma an yi masa aikin dab’i mai inganci. Kamfanin wallafar, bai yi kasa a gwiwa ba, ya yi amfani da takarda mai inganci wajen buga shi, kamar kuma yadda suka yi amfani da kwali mai santsi, mai daukar ido wajen bangonsa. Sai dai duk da wannan tagomashi da littafin ya samu, akwai wasu ’yan kura-kurai da mai nazari zai iya gamuwa da su a littafin. Wannan kuwa yana kara tabbatar da cewa dan Adam ajizi ne, ko kuma kamar yadda masu iya magana ke cewa, tara yake bai cika goma ba.
Wata matsala guda da ta yi ta bayyana cikin littafin, ita ce yadda marubucin kan yi kuskure wajen bayyana lamirin namiji a matsayin mace ko kuma akasin haka. Misali, a shafi na ii, an ce: “kamfanin da ta buga shi” maimakon: “kamfanin da ya buga shi.” A shafi na 6, an ce: “Ga babban talabijin” maimakon: “Ga babbar talabijin.” A Shafi na 22, an ce: “yakin basasa da muka yi fama da ita.” Maimakon: “yakin basasa da muka yi fama da shi.” Irin wadannan sun sha bayyana nan da can a cikin littafin.
Wani abu da ya rage wa littafin daraja shi ne, yadda marubucin ya zabi ya rika amfani da dogayen shedarori wajen bayyana labarinsa. Kamar kuma yadda yake yawan maimaita sunayen taurarin fiye da sau daya a cikin shedara daya. Misali, mu nazarci wannan shedara a shafi na 3:
“Da Amina ta shiga dakinta a sama ba ta yi mamaki ba da ta ga bakuwarta ta farko tana jiran ta a falo. Kulu ita ce matar Sakataren karamar Hukuma, ’yar bizines fitacciya, kuma kawar Amina. Shekarunta sun kai wajen talatin da ’yan kai, ga ta ginanna, kullum saye da tufafi na zamani. Bayan sun gaggaisa sai Amina ta shiga daki ta yiwo kwalliya don tarbar sauran bakin nata: Ta sa bulawus fara da aka yi wa ado da zare mai ruwan gwal, ga gyale fari da ya dace da ita gami da dankwali. Ta sawo zobba na zinari, warawarai na azurfa da ’yan kunne na lu’u-lu’u. Kulu ta tambaye ta ina ta fito da rana haka.”
Wannan doguwar shedara, kamata ya yi a ce an tsinka ta zuwa kashi uku, domin kuwa an cunkushe bayanai daban-daban iri uku. Haka kuma, an ambata sunan Amina har sau uku, a yayin da aka ambata sunan Kulu sau biyu. Wannan yana sanya mai karatu ya gundura, ya ji rashin dadin maida hankali ga karatun. Kamata ya yi a ce idan an ambata sunan mutum sau daya, sai kuma a yi amfani da Wakilin Suna a gaba, musamman ma dai a cikin shedara daya.
Baya ga wannan, akwai kura-kurai da suka yi ta bayyana, musamman ma wajen rubuta wasu kalmomi. Misali, a gaba daya cikin littafin, an yi ta rubuta kalmar: “’yammata” maimakon: “’yan mata.” A shafi na 8, an rubuta: “ga fitulla masu kyau” maimakon: “ga fitilu masu kyau.” A shafi na 10, an rubuta: “kunninsa” maimakon: “kunnensa.” A dai cikin shafin, an rubuta: “ya rakata zuwa ga motarta.” Maimakon: “ya raka ta zuwa ga motarta.”
Haka kuma, wani babban kuskure da aka yi shi ne, inda a cikin littafin, duk inda ya kamata a yi amfani da kalmar: “baki daya” sai ka ga an rubuta: “bakin-ciki.” A nazarina, ina ganin an zo yin gyara daya ne ko biyu, maimakon a bi daya bayan daya, sai aka yi amfani da abin da ake kira “Copy and Replace.” (Wato yadda ake ba kwamfuta ummurnin ta kwafi wata kalma, sannan ta maye gurbinta da wata, a duk cikin littafin.
Duk da wadannan kura-kurai da suka bayyana a littafin, ba su gurbata sakonni da darussan da yake aikawa ga makarancinsa ba. Sai dai ina kira ga kamfanin da ya wallafa littafin, su dabbaka gyare-gyaren kura-kuran da suka bayyana cikinsa, yadda zai zama ingantacce fiye da yadda yake a yanzu.
Game da marubucin littafin ‘Amina’ kuwa, an haifi Mohammed Umar a garin Azare, Jihar Bauchi, Najeriya. Ya yi karatunsa a fannin Jarida da kuma Ilimin Zamantakewa Da Tattali. Yana zaune a garin Criklewood a Ingila, inda yake aiki. Haka kuma ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya a shekarar 1980. Littafin nan, shi ne na farko da ya fara rubutawa.