✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lithium: EFCC ta kama tireloli 3 na ma’adinan hada jirgin sama na sata

EFCC ta kama mutane 10 da tirela uku dauke da ma'adinan Lithium da aka tono ta haramtacciyar hanya

Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) shiyyar Ibadan ta yi wani wawan kamun mutane 10 da suke rakiyar tireloli uku dauke da ma’adinan ‘Lithium’ da aka hako su ta haramtacciyar hanya.

Ana amfani da ma’adanan Lithium wajen hada jiragen sama da batura da magunguna da kuma sauransu.

Kakakin hukumar EFCC, Mista Dele Oyewale ya sanar cewa bayan daukar matakin bin sawu da jami’an hukumar suka yi, sun yi nasarar kama wadannan mutane da motocin a yankin Ogbomoso a Jihar Oyo.

Cikin sanarwar, Oyewale ya ce har zuwa lokacin da aka yi wannan kame, ba a iya gano ainihin inda mutanen suka yi nufin zuwa da wannan nau’in ma’adinin Lithium da aka loda su cikin manyan motocin ba.

Kakakin hukumar ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da mutanen ne gaban kotu domin yanke masu hukumci.