Shugaban Kamfanin Mai na A. A. Rano Nigeria Limited, Alhaji Auwalu Ali Rano, ya ya umarci gidajen mansa kar su sayar da litar man fetur sama da naira 160 ba.
A lokacin da yake jawabi a taron kara wa juna sani kan makamar aiki ga ma’aikatan kamfanin a Jihar Kano, Rano ya ce, sun yanke shawarar sayar da litar mai a kan Naira 158 zuwa 160 domin rage wa ’yan Najeriya matsin da suke ciki.
“Gidajen mai suna sayarwa Naira 162 kowace lita wasu ma har sama da haka. Amma mu a gidajen man A. A Rano da ke fadin Najeriya mun yanke shawarar sayar da shi a kan Naira 160 zuwa 158 domin mu rage wa jama’a radadin da suke ciki
“Amma idan farashi ya canza mu ma za mu duba yiyuwar ragi ko kari duba da gwamnati ta tsame hannunta daga kayyade farashi ba kamar yadda gwamnati ke bayar da tallafi a kan harkar man ba,” inji Auwalu Rano.
Ya ce kamfaninsu ya himmatu wajen fadada kasuwancinsa ta hanyar shiga harkar jiragen sama da na iskar gas sannan zai kaddamar da babban defo na iskar gas a badi.