Masu ababen hawa da al’umma na kokawa kan yadda ake sayar da litar man fetur a tsakanin N400 zuwa N500 a Jihar Edo.
Wakilinmu ya rawaito cewa dogayen layuka sun ki ci sun ki cinyewa a gidajen man da suke sayar da shi a Jihar, lamarin da ya masu ababen hawa suka kara farashin sufuri.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’yan Najeriya suka karbi karin wa’adin tsoffin kudade
- Maganar mutane ba za ta sa na kashe aure na ba – Matar da ta auri saurayin ’yarta
Wani mai abun hawa a Jihar, Michael Abu, ya ce a gidan mai ya kwana, inda ya kyale iyalinsa a gida saboda ya sami man.
“A nan gidan man NNPC na kwana saboda suna sayar da shi a kan N189, yayin da sauran gidajen mai ke sayar da shi a tsakanin N400 zuwa N500. Amma duk da na kwana a nan, ban san lokacin da layi zai zo kaina ba,” in ji Michael.
Shi ma wani mai abin hawan, Celestine Odion, ya shaida wa Aminiya cewa shi ma ya sayi man a kan N400 saboda ba zai iya hakurin kwana a gidan man na NNPC ba.
Ya ce ban da NNPC da ke sayarwa a kan N189, gidajen man Rain Oil da Buvel ne kawai suke sayarwa a kan kasa da N300, inda ya ce tuni suka kara farashin sufuri don ya yi daidai da tsadar man.
Wilson Odia kuwa, wani mai abin hawa a Benin, cewa ya yi tun karfe 5:00 na Asuba ya bar gida da nufin samun man mai sauki, amma bai san lokacin da zai sake shi ba.
“Gaskiya ba zan iya sayen mai a kan N500 ba. Na yanke shawarar in kashe wunin yau na sayi mai sauki, alabasshi na huta a ragowar makon.”
Wata mai amfani da motar haya, Christian Joseph, ta koka da cewa farashin kudin mota daga unguwar Ramat zuwa tashar mota ta Agbor da kuma titin Ring Road, yanzu ya koma N300, N400 da kuma N500, sabanin N150, N250 da kuma N300 da suke biya a baya, saboda tsadar man a yanzu.