✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Litar Fetur Za Ta Haura N400, idan… —NNPC

Sayar da litar man fetur a N170 ba zai yiwu ba, saboda ainihin farashinsa ya kai ninki uku na wannan kudin, in ji shugaban NNPC

Shugaban Kamfanin NNPC, Mele Kyari, ya ce idan aka cire tallafi, farashin dakon litar man fetur kadai zai tashi a N410.

Kyari ya bayyana hakan ne a taron bita ga masu ruwa da tsaki kan lalubo hanyoyin tabbatar da gaskiya da Majlisar Tarayya ta shirya a Abuja ranar Laraba.

“Sayar da litar man fetur a N170 ba zai yiwu ba, saboda ainihin farashinsa ya kai ninki uku na wannan kudin.

“Misali a yau in dai muna so ’yan kasuwa su sayar da litar mai kan N165, to dole ne mu ba su shi a N113.

“Kowa dai ya san yadda farashin mai yake yanzu a kasuwar duniya, amma a Najeriya babu inda za ka sha mai kan N445, mun tabbatar da wannan.”

Da yake jawabi wa taron, wakilin Gidauniyar Konrad-Adenauer ta kasar Jamus a Najeriya, Marji Peran, ya ce a kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna Najeriya na sahun gaba a jerin kasashe marasa tsare-tsaren ciyar da al’ummarsu gaba.

Don haka ya ce akwai bukatar kasar ta kara kaimi wajen tabbatar da ta daidata bangarenta na mai da iskar gas.

Idan za a iya tunawa, a ranar Talata ne ’yan kasuwa suka nemi gwamnati ta ba su damar sayar da man a kan N200 kowacce lita, bayan a jihohin Arewacin Najeriya da dama farashinsa ya haura N200.

 

Daga Itodo Daniel Sule, da Balarabe Alkassim, da Rahima Shehu Dokaji