A ci gaba da kokarin shawo kan matsalar karancin abinci a Najeriya, Kamfanin Tingo Mobile, ya kulla yarjejeniya da Kungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), domin samar da kayayyakin amfanin gona.
Yarjejeniyar wacce aka sanya wa hannu a Abuja ranar Alhamis, za ta bai wa kamfanin Tingo Mobile Plc damar samar da kayayyakin noma irin su iri da, takin zama da takarktoci, hadi da bayar da lamuni ga mambobin Kungiyar AFAN.
- 2023: Dalilinmu na titsiye ’yan takarar Shugaban Kasa —Dattawan Arewa
- Maryam Booth ta zama jakadiyar kamfanin cingam da alawa
Kamfanin zai kuma samar da na’urori masu inganci don tallafa wa kananan manoma don saukaka shiga kasuwanni don sayar da amfanin gonakinsu.
Da yake jawabi yayin taron rattaba hannu kan yarjejeniyar, Shugaban Kamfanin Tingo, Chris Cleverly ya ce hakan zai magance matsalolin karancin abinci a Najeriya.
Haka kuma ya ce akwai bukatar tallafawa manoman karkara da tsare-tsaren yadda da za su bunkasa amfanin gonakinsu, domin magance rashin aikin yi tare da bai wa kananan manoma damar bayar da gudummawa ga cigaban tattalin arziki kasar.
A nasa jawabin, Shugaban kungiyar AFAN, Dokta Farouk Rabiu Mudi, ya ce sabuwar yarjejeniyar za ta ba manoma a faɗin kananan hukumomin Najeriya damar inganta amfanin gonakinsu.
Mudi ya ce yarjejeniyar abin farin ciki ne, musamman a daidai lokacin da manoma ke kir ga asara sanadiyyar ambaliyar ruwa da ta mamaye duniya a bama.