Shugaban Kamfanin NNPC, Mele Kyari, ya ce idan aka cire tallafi, farashin dakon litar man fetur kadai zai tashi a N410.
Kyari ya bayyana hakan ne a taron bita ga masu ruwa da tsaki kan lalubo hanyoyin tabbatar da gaskiya da Majlisar Tarayya ta shirya a Abuja ranar Laraba.
- Al’ummar Filato sun koka kan karuwar mastalar tsaro
- La’eeb: Abin da dan aljanin Gasar Kofin Duniya na Qatar ke nufi
“Sayar da litar man fetur a N170 ba zai yiwu ba, saboda ainihin farashinsa ya kai ninki uku na wannan kudin.
“Misali a yau in dai muna so ’yan kasuwa su sayar da litar mai kan N165, to dole ne mu ba su shi a N113.
“Kowa dai ya san yadda farashin mai yake yanzu a kasuwar duniya, amma a Najeriya babu inda za ka sha mai kan N445, mun tabbatar da wannan.”
Da yake jawabi wa taron, wakilin Gidauniyar Konrad-Adenauer ta kasar Jamus a Najeriya, Marji Peran, ya ce a kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna Najeriya na sahun gaba a jerin kasashe marasa tsare-tsaren ciyar da al’ummarsu gaba.
Don haka ya ce akwai bukatar kasar ta kara kaimi wajen tabbatar da ta daidata bangarenta na mai da iskar gas.
Idan za a iya tunawa, a ranar Talata ne ’yan kasuwa suka nemi gwamnati ta ba su damar sayar da man a kan N200 kowacce lita, bayan a jihohin Arewacin Najeriya da dama farashinsa ya haura N200.
Daga Itodo Daniel Sule, da Balarabe Alkassim, da Rahima Shehu Dokaji