✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Limamin Masallacin Maiduguri Road Kaduna ya rasu

Marigayin da ne ga shahararren malamin addinin Musulunci, Marigayi Sheikh Lawal Abubakar, kuma wa ne ga tsohon Editan Jaridar Daily Trust, Nasiru Lawal Abubakar.

Allah Ya yi wa Babban Limamin Masallacin Maiduguri Raod da ke Kaduna, Malam Dahiru Lawal Abubakar, rasuwa.

Malam Dahiru Lawal Abubakar ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya, a Babban Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna.

Marigayin da ne ga shahararren malamin addinin Musulunci, Marigayi Sheikh Lawal Abubakar, kuma wa ne ga tsohon Editan Jaridar Daily Trust, Nasiru Lawal Abubakar.

Kafin rasuwarsa shi ne Alkalin Kotun Shari’ar Musulunci da ke Karamar Hukumar Makarfi a Jihar Kaduna.

Ya bar duniya yana da shekara 52.

Ana sa ran gudanar da sallar jana’izarsa bayan Sallar Azahar a garin Kaduna.