✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Limami ya kubuta daga hannun ’yan bindiga

Ya tsere a yayinda masu garkuwa da shi ke neman kudin fansa N30m.

Limamin cocin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi a ranar Talata, ya tsere daga hannunsu ranar Lahadi.

’Yan bindigar sun yi awon gaba da Fasto Otamayomi Ogedengbe, Ogedengbe ne a yayin da ake tsaka da ibada a cocin ‘Deeper Life Christian’, da ke Irese a Karamar Hukumar Ifedore ta Jihar Ondo.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun shiga cocin ne cikin wata mota kirar Toyota Corolla suka yi awon gaba da faston.

Daga bisani masu garkuwar suka tuntubi iyalan limaman cocin suna neman kudin fansa Naira miliyan 30.

Sai dai wani makusancin iyalan faston ya tabbatar da kubutarsa, amma ya ce ba shi da tabbacin ko an biya kudin fansan.

Mun tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, Tee-Leo Ikoro, kan lamarin, amma ya ce, “Bani da masaniya a kan lamarin, amma da zarar na samu wani bayani zan sanar da manema labarai.”