✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Limami ya aurar da ’ya’yansa 10 lokaci guda a Borno

Ya bukaci makusantansa da ke zaune a nesa su yi wa ma’auratan addu’a.

Babban Limamin Masallacin Jami’ar Maiduguri, Sheikh Dokta Goni Muhammad Ali Gabchiya, ya bayar da auren ’ya’yansa goma cikin sa’a 24.

A jiya Alhamis ne aka daura auren wasu ’ya’yansa mata biyu yayin da wadansu ’ya’yan nasa mata uku da maza biyar aka daura nasu auren a masallacin Jami’ar bayan sallar Juma’a ta yau.

Daga cikin wadanda suka halarci addu’ar daurin auren har da Shugaban Jami’ar Farfesa Aliyu Shugaba wanda shi ne Waliyyin guda cikin ’yan matan.

Mahaifin wanda fuskarsa cike take ta farin ciki ya ce cikin kwana biyu ya shirya bikin domin gamsar da iyalan bangarorin duka biyu.

Limamin a cikin takardar gayyatar da ya raba, ya bukaci makusantansa da ke zaune a nesa da Maiduguri wadanda ba su iya halartar addu’ar daurin auren da su yi wa ma’auratan addu’a.

Aminiya ta gano cewa angwayen biyar an daura musu auren nasu a gidajen amaren da kowanensu ya aura a yau.