Limaman addinin Kirista a Arewacin Najeriya sun yaba da kokarin Sheikh Ahmed Gumi na nemo dawamammiyar mafita daga matsalar garkuwa da mutane da ayyukan ’yan bindiga da satar dabbobi a Jihar Kaduna.
Shuguban cocin Christ Evangelical, Fasto Yohanna Buru ya ce kokarin shehin malamin da ke shiga dazuka yana ganawa da Fulani makiyaya kan muhimmancin zaman lafiya babban abin yabo ne.
- ‘Yadda muke shiga kunci yayin zaman zawarci’
- An kama limamin da ya daura wa gawa aure a Bauchi
- Sarkin Anka ya mayar da martani kan zarginsa da dakile shirin zaman lafiya
- Gobara ta tashi a masana’antar rigakafin COVID-19
“Allah Zai yi wa malamin sakayya kan lokacinsa da yake warewa yana ziyartar Fulani a dazuka ya ja hankalinsu game da muhimmancin rungumar ilimin boko da Muhammadiyya tare da kiwon dabbobinsu.
“Malamin ya bambanta da takwarorinsa a usulubinsa na neman kawo karshen kashe-kashe da satar dabbobi da garkuwa da mutane da ayyukan ’yan bindiga da sauran hare-hare.
“Wajibi ne a yaba masa saboda jarumtarsa ta tattaunawa da kuma wayar da kan matasan Fulani kan illolin shan miyagun kwayoyi da kuma aikata miyagun laifuka a Jihar.”
Fasto Buru ya kara da cewa, “Saboda muhimmancin zaman lafiya, wajibi ne a rungumi tattaunawa da hadin kai da gwamanti wajen magance matsaloli domin samun cigaban kasa.”
Ya yi kira ga malaman Musulunci da su yi koyi da Sheikh Gumi wurim ware lokaci suna ziyartar al’ummomin Fulani a rugage don ilmantar da su da kuma fahimtar muhimmancin zaman lafiya.
Ya kara da kira ga Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), Majalisar Malamai da Limamai da kuma Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci ta Najeria da su hada kai da Sheikh Gumi wajen yada da’awar zaman lafiya a cikin kauyuka.
Sheikh Gumi na bukatar mataimaka —Rabaran Paul
A nasa bangaren, Rabaran Paul Elisha Ham, ya yi kira ga mawadata da kungiyoyi da kamfanoni da hukumomi da su taimaka wa malamin ta yadda zai ci gaba da yada zaman lafiya a fadin jihohin Arewa 19.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta samar wa malamin matakan tsaro duk sadda zai je yin wa’azi.
Rabaran Paul ya ja hankalin gwamnatin jihar da ta sanya ’ya’yan makiyaya a shirye-shiryen koyar da sana’o’i da kuma ilimantarwa domin rage saman kashe wando.