✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitocin Kano sun kaurace wa asibitin yara na Hasiya Bayero

Likitoci a Jihar Kano sun kaurace wa Asibitin Yara na Hasiya Bayero kan zargin barazana ga rayuwarsu a bakin aikinsu

Kungiyar Likitoci ta Kasa (NMA) reshen Jihar Kano ta umarci membobinta da ke aiki a Asibitin Yara na Hasiya Bayero da su kaurace masa saboda rashin tsaron da ke damun bangaren lafiya a jihar.

Sanarwar da sakataren kungiyar, Dokta Abdurrahman Aliyu ya bayyana cewa a ranar 27 ga watan Mayu 2024, wasu likitoci mata suna aiki suka hadu da tsoratarwa da barazana da gindin bindiga daga wasu mutane ba da suka zo wajen tare da rakiyar masu gadin asibitin.

A cewar sanarwar, “Duk da cewar likitocin sun yi kokarin yi musu bayani, ba su saurare su ba suka ci gaba da kwarara musu ashariya da barazana har da nuna su da bindiga.”

A cewar sanarwar an dauki tsawon awa guda ba tare da an sami wani taimako daga manyan jami’an asibitin ba jamian tsaro da ke wajen asibitin

“Wannan lamari ba shi ne na farko ba da ma’aikatan lafiya ke haduwa da cin zarafi a lokacin da suke bakin aiki a asibitoci.

“Duk da cewa a baya mun yi ta korafe-korafe da roke-roken a kan a kawo mana dauki amma abin ya ci tura.

“Wannan ya nuna cewa rayuwar ma’aikatan lafiya a Asibitin Hasiya Bayero tana cikin hatsari domin ba a dauke ta a bakin komai ba.

“Duk da cewa muna son kula da lafiyar jama’a amma ba za mu iya yi a bakin rayuwarmu ba.

“Yayin da muke neman hadin kan ‘yan uwammu ma’aikatan lafiya, muna neman gwamnati ta yi duba ga harkar lafiya gaba daya domin a yi wa harkar gyara.”

Aminiya ta rawaito labarin wata sanarwa da Shugaba da Sakataren Kungiyar Likitoci suka sanya wa hannu inda suka nuna rashin jin dadinsu game da abubuwan da ke faruwa ga ma’aikatan lafiya a Kano.

A farkon shekarar nan wasu matasa dauke da muggan makamai suka kai hari kan wani ma’aikacin lafiya yana cikin aiki a bangaren masu haihuwa a Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed.

Yayin da Aminiya ta tuntubi kakakin Hukumar Asibitocin Jihar Kano, Samira Sulaiman, wadda ta bayyana cewa hukumar na sane da abin da ya faru a Asibitin kuma ta fara gudanar da bincike, da zarar an kammala za ta sanar da wakiliyarmu halin da ake ciki.