✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitoci sun tsunduma yajin aiki a Najeriya

Likitoci sun kafa wa Gwamnatin Tarayya sharudan janye yajin aikin.

Kungiyar Likitocin Najeriya (NARD), ta sanar da shiga yajin aikin sai baba ta gani, kan rashin inganta musu ayyuku da rashin kuma biyan hakkokinsu da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Kungiyar na kasa, Dokta Uyilawa Okhuaihesuyi yayin zantawarsa da Kamfanin Dillacin Labarai NAN a ranar Alhamis.

“Mun fara yajin aikin da misalin karfe 8 na safiyar Alhamis bayan zama biyu da muka yi da gwamnati.

Mun yi zama na farko a ranar 31 ga Maris da Shugaban Kwamitin Majalisar Koli kan harkar kiwon lafiya, Dokta Ibrahim Yahaya, don fahimtar juna.

“Dayan kuma mun yi da Ministan Ayyuka, Mista Chris Ngige da karfe 4 na yammacin ranar Laraba, inda ya gabatar mana da takardar yarjejeniya, sai dai muna bukatar tattaunawa a kungiyance tukunna.

“Ni dan aike ne, ina yin aiki na ne kuma a bisa tanadin kundin tsarin NEC, don haka za mu kai sako ga kungiya don ganin matakin da ya dace a dauka,” a cewar Okhuaihesuyi

Sannan ya kara da cewa dole ce ta sanya suka shiga yajin aikin, saboda gazawar gwamnati na cika alkawuran da ta daukar musu a baya.

“A baya an kulla yarjejeniya da dama da gwamnati, amma ta gaza cika alkawarin da ta dauka,” a cewarsa.

Kazalika, kungiyar ta ce dole ne gwamnati ta cika alkawuran da ta daukar musu kafin su janye yajin aikin.

Daga ciki akwai bukatunsu akwai biyansu albashin watan Maris, da kudaden alawus na yaki da cutar COVID-19, sai kuma sauran hakkokinsu da aka gaza biya musu.