Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa (NARD) ta janye zanga-zanar gama-garin da ta shirya shiga a fadin Najeriya a yau Laraba.
Shugaban kungiyar, Dokta Orji Emeka Innocent, ya ce majalisar kolin kungiyar ta yanke shawarar ne bayan taron da ta yi ranar Laraba da dare.
- Kwankwaso ba sa’anka ba ne a siyasance – NNPP ga Ganduje
- ECOWAS ta sake kakaba wa Nijar sabon takunkumi
Sai dai ya ce cikin sa’o’i 72 masu zuwa kungiyar za ta sake zama ta kara nazari kan matakin janye zanga-zanar.
Da farko NARD ta shirya gudanar da zanga-zanga a kullum ta hanyar rufe cibiyoyin lafiya mallakin gwamantin tarayya daga karfe 10 na ranar Laraba 9 ga watan Agustan nan da muke ciki.