Likitoci sun shiga kakabi bayan sun gano daruruwan tsabar kudi da kusoshi da batura da guntattakin gilasai bayan dawani mutum mai suna Burhan Demir daga garin Ipekyolu na kasar Turkiyya ya kai kaninsa asibiti saboda kukan ciwon ciki.
A lokacin da likitocin suka yi gwajin hoton cikin mutumin ta amfani da endoscopic tare da daukar hoton cikin da na’urar d-ray sun yi mamaki bayan gano abubuwa 233 a cikin mara lafiyar mai shekara 35.
- An nada kasurgumin dan bindiga sarautar gargajiya a Zamfara
- Amfanin ganyen ‘aloe vera’ wajen gyara jiki
Abubuwan sun hada da tsabar karafan kudin kasar Lira guda daya da batura da mayen karfe da kusoshi da gilasai da duwatsu.
Daga baya likitocin sun cire abubuwan da suke cikin majinyacin, mai suna Z, kawai.
Wani likitan fida – mai suna Dokta Binici – ya ce: “A lokacin tiyatar, mun ga daya ko biyu daga cikin kusoshi sun bi ta bangon cikinsa.
“Mun gano cewa a cikin babban hanjinsa akwai karafuna biyu da duwatsu biyu masu girma daban-daban.
“Mun gano cewa akwai batura da mayen karafe da kusoshi da tsabar kudi da guntayen gilasai. Mun cire bakin abubuwan daga cikinsa gaba daya.
“Ba yanayin da muke gani a manya ba ne, yawanci a cikin yara ne da suke hadiye abubuwa ba tare da saninsu ba. Ana iya ganin hakan a cikin marasa lafiya masu tabin hankali ko fursunoni ko wadanda ake cin zarafinsu a cikin rukunin manya,” inji shi.
Burhan ya shaida wa kafafen yada labarai na kasar cewa: ‘An kai kaninsa wannan asibiti ne bayan binciken lafiyarsa da aka yi, an yi masa tiyata aka cire wadannan abubuwa daga cikinsa.
Ba a dai bayyana lokacin da aka gudanar da aikin ba, amma an bayar da labarin a kafafen yada labarai na kasar a ranar 15 ga watan Yunin bana.
Burhan ya kara da cewa: “Na gode wa likitocin saboda kulawa da goyon bayansu.”