✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitoci na bincikar lafiyar Jami’in da ya nemi a bashi jan ragamar Hukumar Kwastam 

Hukumar Kwastam ta yi karin haske game da jami’in ta Nura Dalhatu Wowo da ya yi wa kansa karin girma ya nemi a bashi ragamar…

Hukumar Kwastam ta yi karin haske game da jami’in ta Nura Dalhatu Wowo da ya yi wa kansa karin girma ya nemi a bashi ragamar Hukumar.

A sakon da Mai magana da yawun Hukumar ta kasa Joseph Attah, ya fitar ya bayyana cewa jami’in ba ya cikin hayyacin sa, ya ce an gayyato likitoci wadanda ke aikin bincikar lafiyarsa

Bayanai sun tabbatar da cewa, tun a ranar 13 ga watan Mayu jami’in Nura Dalhatu mai anini biyu ya rubuta a Shafinsa na Facebook cewa, shugaba Buhari ya tabbatar da nadinsa a matsayin wanda zai ja ragamar Hukumar Kwastam bayan shugabanta na yanzu CGC Hamid Ali, ya ajiye aiki.

Wasu jami’an Kwastam da ke aiki a babban ofishin Hukumar da ke Abuja sun shaida cewa, manyan jami’an rundunar sun yi ta sarawa Nura Dalhatu Wowo, cikin rashin sani domin sun dauka mukaddashin shugaban rundunar ne a lokacin da ya tunkari ofishin shugabar Hukumar da zunmmar ayi masa handin oba ya kama aiki gadan-gadan.