✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitoci da wanzamai, danjuma ne da danjummai- Sarkin Askan Rigasa

A ranar Alhamis din makon jiha ne Hikimin Gundumar Rigasa ya  nada Malam Muhammadu Lawan Abdullahi Sarkin Askan Gundumar Rigasa. A wannan zantawa da Aminiya…

A ranar Alhamis din makon jiha ne Hikimin Gundumar Rigasa ya  nada Malam Muhammadu Lawan Abdullahi Sarkin Askan Gundumar Rigasa. A wannan zantawa da Aminiya ya bayyana  mahimmacin sana’ar wanzanci ga rayuwar dan Adam inda ya ce ai wanzamai su ne likitocin farko.

Me za ka ce dangane da sarautar Sarkin Aska da aka yi maka?
Ina jin farin ciki fiye da kima domin farin cikin da nake ji sai ka ce a yau aka haife ni.

Shekara nawa ke nan da ka fara sana’ar aski?
Zan iya cewa zan kai kamar shekara arba’in da biyar. Kuma na fara zama ne a Tudun Wada kafin daga baya na dawo cikin Rigasa.

Me za ka ce game da wannan sana’a taku ta wanzanci?
Alhamdulillahi sai dai godiya ga Allah a kan wannan sana’a tamu, domin muna yin sana’ar ne a matsayin taimako. Duk wanzami sana’arsa taimako ne. Tun da za a ba shi abu kadan ya ce ya gode Allah Ya sa albarka, sai kuma Allah Ya sa abubuwansa su yalwata komai ya tafi masa daidai.

Gadar sana’ar ka yi ko kuwa haye ka yi mata?
Gadarta na yi daga mahaifina Malam Abdullahi.

Ko iyalanka nawa a yanzu?
Matana uku kuma ina da ’ya’ya goma sha uku.

Ko daga cikin ’ya’yanka akwai wadanda suke gaje ka?
kwarai kuwa, akwai hudu wadanda ke wannan sana’a. Sadiku da Jibril da Aliyu sai kuma Salisu.

Idan aka yi la’akari da yadda zamani ya sauya kamar yanzu wanzanci na samun koma-baya, ko mene ne kake ganin ya jawo hakan?
A tsakanin matasa ka san abubuwa na tafiya ne da zamani yadda zamani ya juya ake binsa. Mu dai mun ga abin da iyayenmu ke yi kuma a yanzu shi muke yi, kuma ’ya’yanmu suna ganin abin da muke yi. Muna nuna musu cewa wanzami a ba shi kadan ya ce ya gode arzikinsa ke nan. A ba shi ya ce ya raina tsiyar wanzanci kenan. Amma idan aka ba ka, ka ce Allah Ya sa albarka to, abarka za ta bi ka.

Ka shafe shekaru masu yawa a wanzanci, ko akwai wani abin alheri da ka samu dalilin wannan sana’a?
Ai na gama samun alheri tun da duk matan da na aura da ‘ya’yan da na samu a dalilin wannan sana’a na same su. Ka ga kuwa ai na gama samun alheri sai karashe.

Ko wace rawa ka taka wajen koya wa matasa wannan sana’a?
‘Ya’yana matasa ne kuma na koya musu sana’ar ka ga ai shi ke nan. Su kuma sai su ci gaba da koya wa abokan huldarsu. Abin da farin cikin shi ne sun gada kuma suna yi.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci nadin sarautarka har da mataimakin shugaban kungiyar wamzamai ta jiha. Me za ka ce?
Na yi matukar farin ciki sakamakon halartar da ya yi, saboda a kullum yakan fada mana cewa mu ci gaba da hakuri, mu kuma rike ’yan uwanmu, sannan mu hada kanmu. Kuma yana kokarin shiga lunguna wajen fadakar da ’yan kungiyarmu.

Mene ne abin da ya fi bata maka rai dangane da wanzanci?
Ni dai a sana’ar nan ko an bata min rai ban sani ba. Tun da zan yi aikina lafiya lau kuma duk abin da aka ba ni nakan ce na gode, to me zai bata mini rai. Babu wani abu da zan ce an yi mini da ya bata min rai. Duk tufafin da na sanya a sana’ar nanna same su, kuma kana maganar farin ciki tun da har na fada maka cewa aure da na yi duk da wannan sana’a na yi ai karshen farin ciki ke nan.

Wane jan hankali za ka yi ga matasan kasar nan domin su rungumi sana’a?
Matasanmu su rungumi sana’a, sannan su rike ta tsakani da Allah. Kada su ha’inci ’yan uwansu kuma duk abin da suka rike tsakani da Allah, to Allah zai taimake su.
Kuma abin da muke fada musu shi ne suke rike sana’ar nan tsakani da Allah, Allah zai taimaka masu. Yanzu duk inda ka ga wanzami ba ka ganinsa cikin kazanta. Kuma mu ne likitocin farko. ’Yan boko ne suke kwace mana sana’a wai su likitoci. Likitocin ma mun zauna da su kuma akwai likitan da na zauna da shi a ofishin Hakimi. Na nuna masa cewa askar da suke aiki da ita mu ma mun iya aiki da ita wajen kaciya. Hakan ya sa ya ba ni kwali uku na aska, ya kuma ba ni sabulun Dettol kwalba hudu, saboda na nuna masa ya kuma gamsu da irin tsaftarmu. Saboda haka na ce masa da mu da su likitoci so muke mu rungumi juna. Abin da muka ga ba za mu iya ba dole a je wajensu. Su Kuma wanda ba za su iya ba dole a zo wajenmu domin neman taimako.
Kamar mataimakin shugaban kungiyar mu ta jiha idan ka kai masa mace mai cutar kansa sai ya warkar da ita. Daga asibiti ma suna kai masa kuma a dace. Saboda haka mu ma likitoci ne. Muna kuma nuna wa ‘ya’yanmu cewa su rika tsafta in za su fita su wanke kayansu domin su yi tsaf yadda kowa ya gan su zai yi sha’awarsu.