✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Likitoci 15 sun kamu da cutar Coronavirus a Jihar Nasarawa

Likitoci 15 daga cikin 139 da ke aiki a Asibitocin Gwamnatin Jihar Nasarawa sun kamu da cutar Coronavirus. Babban Daraktan Asibitin Kwararru na Dalhat Ashraf,…

Likitoci 15 daga cikin 139 da ke aiki a Asibitocin Gwamnatin Jihar Nasarawa sun kamu da cutar Coronavirus.

Babban Daraktan Asibitin Kwararru na Dalhat Ashraf, Dokta Ikrama Hassan ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Lafia, babban birnin Jihar.

Ya sanar cewa, “Ikirarin da Kungiyar Likitoci ta Jihar ta yi na cewa Likitoci 35 sun kamu da cutar Coronavirus ba daidai bane, sai dai tabbas Likitoci 15 sun harbu.”

“Ina rokon kada su shiga wani yajin aiki domin taimakon al’umma, amma ina kira da su nemi a tattauna kan bukatunsu.”

“Idan an samu wasu ma’aikata uku da suka kamu da cutar a wani sashi na asibitin, ina dalilin rufe wasu sassan da ba a samu ko ma’aikaci daya da ya kamu ba.”

“Asibitin nan ya tanadi duk wasu kayayyakin kariya, saboda haka babu ma’ana Likitoci su tsunduma wani yajin aikin ana tsaka da fuskantar zagaye na biyu na wannan annoba,” in ji Dokta Ikrama.

Kazalika, a makon jiya ne Gwamna Abdullahi Sule ya sanar da cewa mutum hamsin sun kamu da cutar ranar Lahadi kadai a fadin Jihar.

Ya bayyana hakan ne a fadar gwamnatinsa da ke birnin Lafia yayin wani taro tare da Shugabannin Kananan Hukumomi 13 na Jihar da kuma masu ruwa da tsaki.

A cewarsa, “a wannan zagaye na biyu na annobar Coronavirus, an samu mutum 50 da suka harbu a ranar Lahadi, wanda wannan shi ne adadi mafi yawa da aka taba samu rana guda a Jihar tun bayan bullar cutar.”

“Ina kira ga al’ummar Jihar da su sake sabunta taka tsan-tsan wajen kiyaye dukkanin ka’idodin kariya da aka gindaya domin dakile yaduwar cutar,” inji Gwamnan.

Gwamna Sule ya yi gargadin cewa har yanzu annobar cutar tana nan a tsakanin al’umma duba da yadda ake ci gaba da samun babban kaso na mutanen da ke kamuwa da cutar a Jihar.

A karshen watan Dasumba na shekarar da ta gabata ne Mataimakin Gwamnan Jihar kuma Shugaban Kwamitin Yaki da Cutar Coronavirus a Jihar, Dokta Emmanuel Akabe, ya sanar cewa cutar ta yi ajalin mutum 15 a fadin Jihar.

A cewarsa, “ya zuwa ranar Talata, 22 ga watan Dasumba, an sallami mutum 668 da suka warke daga cutar Coronavirus kuma kaso 85 cikin dari na wadanda suka harbu sun fito ne daga Kananan Hukumomin Karu, Keffi da kuma Lafiya a yayin da sauran wadanda suka kamu suka fito daga ragowar Kananan Hukumomi 10 na Jihar.”

Mataimakin Gwamnan ya kuma sanar cewa, Dokta Rebecca Isaac Umaru, tsohuwar Shugabar Kwalejin Ilimi ta Akwanga ta mutu ne a sakamakon cutar a ranar Litinin, 21 ga watan Dasumba.

Ya kuma ce Dokta Janet Angbazo, Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Labarai, Al’adu da Yawon Bude Ido, ita ma ta kamu da cutar inda a halin yanzu an killace ta.

A cewarsa, akwai kuma wani mai yiwa kasa hidima da aka gano yana dauke da kwayar cutar a birnin Lafia.

Ya ce, wannan zagaye na biyu na annobar babban abin damuwa ne duba da yadda ta fi tsanani a wannan karo fiye da yadda ta kasance a baya.

Dokta Akabe ya ce alkaluman da gwamnatin ta samu sun nuna cewa a wannan karo hatta masu kananan shekaru ba su tsira ba duba da yadda cutar ta kara tsananta.

Da wannan ne ya yi kira ga al’ummar Jihar da su dage wajen sanya takunkumin rufe fuska, bayar da tazara da yin nesa-nesa da juna, wanke hannu a kai a kai domin dakile yaduwar cutar.