Dubun wani korarren dalibin jami’a da ya zama likitan bogi ta cika inda aka kama shi a wani asibiti mai zaman kansa a Jihar Gombe.
Likitan bogin mai shekara 36, wanda dan asalin garin Ekpoma na Jihar Edo ne, ’yan sanda sun cafke shi ne a yayin da yake tsaka da duba wani mara lafiya.
- ’Yan Najeriya da suka kamale a Ukraine za su iso gida ranar Alhamis
- Muhimman abubuwa 10 da ’yan Najeriya ke cewa a kan sabuwar dokar zabe
Ma’aikatan asibitin ne suka gano rashin kwarewarsa sannan suka sanar da hukumar gudanarwar asibitin.
A kan haka ne shugaban asibitin ya sa aka bincika aka gano cewa likitan bogin bai iya aiki yadda ya kamata ba.
Daga baia sai aka neme shi domin a tantance takardunsa domin gano matakin kwarewarsa a kan aikinsa.
Bayan gudanar da bincike a hukumar yi wa asibitoci lasisi ta kasa NMC, asirinsa ya tonu, aka gano cewa takardun da yake amfani da su ba nasa ba ne. Nan take kuma suka kai wa ’yan sanda kara.
Da ya ke gabatar da likitan bogin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, Babatunde Ishola Babaita, ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa shi ba likita ba ne, da takardun shaidar kammala karatun bogi yake amfani.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, wanda ake zargin ya ce matsin rayuwa ne ya sa shi aikata hakan.
A cewasa, yana da ilimin aikin likitanci daidai gwagwado domin a baya shi dalibin jami’a ne mai karatun aikin likita, amma saboda wasu matsaloli aka kore shi daga jami’a.
Ya kara da cewa ya yi nadamar abin da ya aikata, yana naman a yafe masa saboda kuncin rayuwa ne ya sa shi aikata hakan.
Kwamishinan ’Yan Sandan ya ce da zarar an kammala bincike a kansa za su tura shi zuwa kotu domin yanke masa hukunci.