✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Liki A Wajen Biki Ya Sa EFCC Garkame Wata A Gombe

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki kasa (EFCC) ta tsare wata mata da ta yi likin kudi a wurin bikin a Jihar Gombe

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki kasa (EFCC) ta tsare wata mata da ta yi likin kudi a wurin biki a Jihar Gombe.

Ofishin Shiyyar Arewa maso Gabas na hukumar ya ce ya kama matar ne bisa zargin ta da wulakanta Naira a wajen taron bikin.

Jami’an EFCC sun kama matar da ake zargin ne bayan fitan wani faifan bidiyo a ranar 20 ga Watan Mayu 2024 tana lika Kudi a bainar jama’a.

Wacce ake zargin mai suna Janty Emmanuel da aka nuna mata faifan Bidiyon tana liki a wani dakin taro mai suna G-Connect da ke unguwar Tumfure, ba musu nan take ta amince da zargin.

Sannan hukumar ta EFCC ta bayyana cewa nan gaba kadan da zarar sun kammala bincike a kai ta za su gurfanar da ita a gaban kotu.