Dan kwallon kulob din Leicester City na Ingila kuma daya daga cikin ’yan kwallon Super Eagles ta Najeriya, Wilfred Ndidi watakila ya canza sheka zuwa kulob din Liberpool na Ingila a karshen kakar wasa ta bana kamar yadda jaridar Mirror ta Ingila ta kalato a farkon makon nan.
Ndidi dan shekara 21, ana sa ran zai maye gurbin dan kwallon tsakiya a kulob din Liberpool kuma haifaffen kasar Jamus Emre Can da ake ganin zai bar kulob din a karshen kakar wasa ta bana.
Ndidi wanda tauraruwarsa ke haskakawa a kulob din Leicester bayan da ya koma kulob din daga Genk a watan Janairu, 2017 yana cikin ’yan kwallon da za su yi wa Najeriya kwallo a yau Juma’a da kasar Poland a wasan sada zumunta.
Kawo yanzu ya buga wa Najeriya wasa sau 14 bayan da aka fara gayyatarsa a shekarar 2016 sannan ya buga wa kulob din Leicester City wasanni 30 kawo yanzu a kakar wasa ta bana.