Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili. Da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin:
Tambaya: Ni dai muna zaune lafiya da mijina; yana kyautata min daidai gwargwadon hali; matsalata daya da shi, ita ce yana da masifar son ’yan mata; musamman ’yan matan waya; domin in na duba wayarsa nakan ga irin kazamar hirar da yake yi da ’yan matansa ta kafofin sada zumunta irin su Facebook da WhatsApp.
Idan kuma na tunkare shi da maganar sai ya ce min ba haka ba ne zargi ne kawai nake yi. Don Allah Duniyar Ma’aurata ku ba ni shawara, yaya zan yi in magance wannan matsala?
Daga Mai Neman Shawararku:
Wannan fili yana yawan samun iren-iren wadannan sakonni daga ’yan uwa mata suna neman mafi kyan hanya ta warware wannan babbar matsala da ta fado masu cikin rayuwar aurensu; don haka ga cikakken bayanin da zai amsa dukkan tambayoyinku masu nasaba da wannan matsala da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa musamman wadanda suka aiko da tambayoyin, amin.
Leken sirrukan wayar maigida:
Yakan faru ne lokacin da uwargida ta faki idon maigidanta ta dauki wayarsa ta duba sakonni, hotuna da lambobin da ya kira da niyyar tabbatar da wani abu da take zargi game da dangantakarsa da mata a waje, a dalilin wasu alamu da ta lura da su game da shi wadanda suka haifar da zargi a cikin zuciyarta.
Wadansu matan auren, leken sirrin wayar maigidansu ya zame masu jiki ta yadda koyaushe a fakaice suke da zarar ya bar wayarsa su dauka su duba abin da suke so cikin sauri su mayar su aje.
Wadansu kuma yanayi ne ke kai su ga wayar maigidansu kuma har su ci karo da abin da ba su zata ba kuma abin da zai bata masu rai.
Misalin haka kamar matar da mijinta ya ba ta aron wayarsa, a dalilin haka ta ga kazaman sakonnin da suka yi musaya tsakaninsa da ’yan matansa.
Boye sirri tsakanin ma’aurata:
Shin ya kamata boye sirri tsakanin ma’aurata? Wannan ya danganta da yanayin dangantakar da ke tsakanin ma’aurata, wadansu ma’auratan akwai kyakkyawar dangantaka da aminci a tsakaninsu ta yadda ba sa boye komai ga junansu; a irin haka idan mace ta duba wayar maigidanta bai zama leken asiri ba domin a gabansa ma tana iya yin haka.
Wadansu ma’auratan kuwa komai kyan dangantakarsu ba sa yarda su saki sirrinsu ga juna. Magidanta maza sun fi boye sirrin wayarsu ga matansu; saboda wani sakon ko da ba abin zargi ba ne, wadansu matan idan sun gani suna iya mai da shi abin zargi har ya zama sanadiyyar faruwar matsala tsakaninsu da mazansu.
Wadansu kuma na boyewa ne saboda sun san akwai sakonnin ’yan matansu da ba su son matan aurensu su gani.
Aure wani babban al’amari ne da yake halatta bayyanuwar dukkan sirri ga wanda mutum yake aure; haka kuma wani al’amari ne da ke hade mutum biyu su dunkule su zama daya, ba iyakancewa ta zahiri ko badini.
Don haka idan kyakkyawar danganta ta kullu a tsakanin ma’aurata, ya kamata a ce ba wani boye sirri a tsakaninsu. Rashin yarda da amincewa da juna shi yake sa ma’aurata su rika boye sirrin junansu.
Kuma shi yake sa su rika zargin juna har ya kai ga dayansu ya rika leken sirrin dayan. Sannan bambanci a tsakanin mutane ya sa wadansu mutanen suka dauki boye sirri da muhimmanci sosai ta yadda ba sa son kowa ya duba wayarsu ko da kuwa mata ko mijin da suke aure ne, kuma ko da babu wani abin boyewa a ciki.
Wadansu kuwa ba su damu ba, ko ma wane ne ya buda ya ga duk abin da ke ciki ko da kuwa akwai abin zargi a ciki.
Leken sirri ta mahangar addini:
Allah Madaukakin Sarki Ya hani dukkan Musulmi ya yi leken asiri ga dan uwansa; wannan ya kunshi har miji da mata.
Kamar yadda ya zo a cikin aya ta 12, cikin Suratul Hujurat: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku nisanci abu mai yawa na zato; lallai wani sashe na zato laifi ne.
“Kuma kada ku yi leken asirin juna, kuma kada sashenku ya yi gibar sashe, shin dayanku zai so ya ci naman dan uwansa matacce? Ba za ku so haka ba,(cin naman, don haka ku ki giba).
“Kuma ku bi Allah da takawa, lallai Allah Mai karbar tuba ne, Mai jinkai.”