✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Leicester City ta sanya Kelechi Iheanacho a kasuwa

Kulob din Leicester City da ke buga gasar firimiyar Ingila ya ce ya fara yunkurin sayar da dan kwallon gabansa dan asalin Najeriya Kelechi Iheanacho.…

Kulob din Leicester City da ke buga gasar firimiyar Ingila ya ce ya fara yunkurin sayar da dan kwallon gabansa dan asalin Najeriya Kelechi Iheanacho.

Kelechi wanda kulob din ya saye shi a farkon kakar wasa ta bana, yanzu ya yi nadamar sayo dan kwallon ganin bai tabuka abin a-zo-a-gani.  Kawo yanzu dan kwallon ya buga wasanni biyu ne kacal tun bayan komawarsa kulob din.

Mahukunta kulob din su nuna ko da za su yi asara ne, sun gwammabe su sayar da dan kwallon maimakon su kyale shi ya rika karbar albashin Fam dubu 155 kwatankwacin Naira miliyan 73 a duk mako.

Kulob din ya kara da cewa kulob da dama sun nuna sha’awarsu a kan Kelechi amma da sun ji yadda yake karbar albashin Fam dubu 155 sai su yi kwana, su fasa cinikin. A kan haka ne kulob din Leicester yake neman rabuwa da Kelechi Iheanacho ko ta halin kaka hasalima ko da zai yi asarar a cinikin dan kwallon ne.

Iheanacho dai yana daga cikin ’yan kwallon Najeriya Super Eagles da ake sa ran zai halarci gasar cin kofin duniya ta bana a Rasha a watan Yuni.