✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Leicester City ta kori kocinta

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Leicester City na Ingila ya bayyana sanarwar korar kocinsa Craig Shakespeare watanni hudu kacal bayan an…

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Leicester City na Ingila ya bayyana sanarwar korar kocinsa Craig Shakespeare watanni hudu kacal bayan an nada shi a matsayin koci.  Kocin wanda ya sanya hannu a kwantaragin shekara uku, yanzu kulob din ya  sallame shi ne saboda rashin kokari a kakar wasa ta bana.

Tun bayan da kocin ya fara horrar da kulob din ya samu nasara ne a wasanni takwas kacal daga wasanni 16 da ya yi al’amarin da ta sa yanzu haka kulob din ne na 17 a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar rukunin firimiyar Ingila.

Kulob din ya dauki matakin sallamar kocin ne jim kadan bayan an tashi wasa a tsakanin kulob din da West Brom a ranar Litinin inda aka buga kunnen doki 1-1 a gasar rukunin firimiyar Ingila.