Leeds United ta kammala ɗaukar ɗan wasan bayan ƙungiyar Udinese na ƙasar Slovenia, Jaka Bijol mai shekaru 26 kan farashin fam miliyan 15.
Wannan dai shi ne sabon ɗan wasa na biyu da ƙungiyar ta ɗauka bayan zuwan ɗan wasan gaban Jamus, Lukas Nmecha, kyauta.
- ‘Harin da Iran ta kai wa sansanin sojin Amurka keta haddin Qatar ne’
- Iran ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka
Cefanen Bijol da Leeds ta yi zai ƙara wa ƙungiyar tagomashi wajen tsaron bayanta a yayin da ake shirye-shiryen dawowa sabuwar kakar wasanni ta Firimiyar Ingila.
Bijol dai ya buga ƙasarsa Slovenia wasanni 63 ciki har da rawar gani da ya taka a gasar Euro 2024, inda suka yi canjaras da Ingila a wasannin cikin rukuni gabanin rashin nasara a hannun Portugal yayin bugun daga kai sai mai tsaron raga daf da tafiya matakin kwata-fainal.
Bijol ya shafe kaka uku a yana taka wa Udinese leda a gasar Serie A, inda ya haska a wasanni 95 bayan dawowarsa ƙungiyar ta Italliya daga CSKA Moscow, inda ya shafe shekaru hudu.
Leeds dai ta samu nasarar haurowa Firimiyar Ingila a watan Mayun da ya gabata, bayan ta karkare gasar Championship ta maki 100 daidai da Burnley wadda ta bai wa rata da kwallaye.
AFP