Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta cefano dan wasan gaba na Brazil Raphinha daga Leeds United a kan farashin da ya kai fam miliyan 55 (£55m).
An gabatar da dan wasan, mai shekara 25, ga magoya bayan kungiyar a filin wasan Catalan ranar Juma’a.
- Kotu ta daure Fasto shekara 10 saboda yi wa ’yar shekara 14 fyade
- ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a Filato
Raphinha, wanda ya koma Leeds daga kungiyar kasar Faransa Rennes a kan fam miliyan 17 (£17m) a 2020, ya murza leda sau 65 a gasar Firimiyar Ingila a kungiyar ta Yorkshire club, inda ya ci kwallo 17 sannan ya taimaka aka ci 12.
Da yake jawabi ga dimbin magoya bayan da suka yi cikar kwari wajen gabatar musu da shi a matsayin sabon dan wasan kungiyar, Raphinha ya ce, “tun ina karamin yaro nake burin zuwa wannan kungiyar.
“Zan yi bakin kokarina.”
Leeds United ta yaba wa Raphinha a sanarwar da kungiyar ta fitar yayin da take tabbatar da rabuwa da dan wasan: “Muna son tarihi ya sani cewa muna mika godiyarmu ta musamman ga Raphinha saboda da gudunmawar da ya bai wa kungiyar ta kwallon kafa.
“Ya zage dantse sosai har zuwa lokacin da ya kammala zamansa a Elland Road kuma gudunmawarsa a filin wasa na Brentford ba za ta gushe daga tunaninmu ba.”
Ana iya tuna cewa, Raphinha ne ya ci fenaretin da Leeds ta yi nasara da ci 2-1 a karawarsu da Brentford a ranar karshe a kakar wasa ta 2021/22, lamarin da ya sa suka samu gurbi a Firimiyar ta bana.