✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Laycon ya zama zakaran shirin BBNaija na 2020

Olamilekan Moshood Agbelese, wanda aka fi sani da Laycon ya zama gwarzon shirin talabijin na BBNaija karo na biyar na shekarar 2020. Laycon wanda  ya…

Olamilekan Moshood Agbelese, wanda aka fi sani da Laycon ya zama gwarzon shirin talabijin na BBNaija karo na biyar na shekarar 2020.

Laycon wanda  ya kammala digirinsa a Jami’ar Legas a fannin nazarin halayyar dan adam ya sami nasarar ne bayan ya lashe kaso 60 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada.

A sakamakon haka, zakaran shirin na bana zai tafi gida da kyaututtukan da darajarsu ta kai ta kusan Naira miliyan 80.

Dorothy ce dai ta zo ta biyu bayan ta sami kaso 21 cikin 100 na kuri’un, yayin da Nengi, Neo da Vee suka zo na uku, na hudu da na biyar.

Kyaututtukan dai da Laycon ya lashe kamar yadda masu tsara shirin suka bayyana sun hada da tsabar kudi Naira miliyan 30, gida mai dakunan kwana biyu, mota kirar SUV jif, tafiya zuwa biranen Dublin da Dubai, kayan lantarki na gida da kuma taliyar Indomie wacce zai ci ta tsawon shekara guda.

Sauran kyautukan sun hada da man goge baki na Colgate, lemon kwalba na Pepsi wanda zai sha na tsawon shekara guda, tafiya domin kallon wasan karshe na gasar zakarun Turai da kuma sabuwar wayar alfarma kirar kamfanin Oppo.

Tun dai lokacin da aka ayyana shi a matsayin zakaran na bana, magoya bayan Laycon suke ta bayyana farin cikinsu musamman a shafin Twitter da ma sauran kafafen sada zumunta na zamani.