✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Lauyoyin gwamnati za su sayi rigunan N258m —Malami

Ministan Sharia'a ya ce ana biyan lauyoyin kudaden sayen alkyabbar aikinsu.

Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya ta ce tana kashe Naira miliyan 258 wajen biya lauyoyinta 860 alawus din sayen alkyabbar aikinsu.

Ministan Sharia’a kuma Antoni-Janar na Tarayya, Abubakar Malami, shi ne ya bayyana haka a yayin da yake kare kasafin kudin ma’aikatar na 2022 a gaban kwamitin Majalisar Dattawa.

Malami ya yi bayanin ne bayan Sanata Emmanuel Orker-Jev ya diga ayar tambaya a kan yawan kudaden albashi da alawus-alawus din ma’aikatar da lauyoyinta.

Ma’aikatar dai ta gabatar da kasafin Naira biliyan 11.3, wanda daga ciki aka ware Naira biliyan 8.2 domin biyan albashi da alawus din ma’aikata da kuma ayyukan yau da kullum.

Da jin bayanin Malami ne Sanata Emmanuel ya ce, “Na fi shekara 10 ina amfani da alkyabba daya.” 

Sai dai Shugaban Kwamitin, Sanata Opeyemi Bamidele, ya katse masa hanzari da cewa alawus din zai tabbatar da ganin lauyoyin na yin kyakkyawar shiga tsaf-tsaf a gaban kotuna.