✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lauya ya ’yanta fursunoni 6 a Gombe

Lauyan ya yi kira ga sauran masu hannu da shuni da su ma su bi sahu.

A kokarinsa na ganin an rage cunkoso a gidajen yari a Najeriya, wani lauya mai zaman kansa a Jihar Gombe, Barista Musa Jibrin Biri ya ’yanta fursunoni shida a Jihar.

Lauyan, wanda ke fafutukar kare hakkin dan Adam ya ce lokaci ya yi da alkalai za su fara yanke hukuncin aikatau ga masu laifukan da ba su taka kara sun karya ba, a maimakon kai su gidajen yari don rage cunkoso.

Barista Musa Biri ya ce hakan zai taimaka matuka wajen rage cunkoson, musamman ganin yadda ake fama da cututtuka daban-daban da ke barazana ga rayuwar al’umma.

Lauyan ya kuma yi amfani da damar wajen shawartar masu hannu da shuni da kungiyoyin al’umma masu zaman kansu da su taimaka wajen biyan tara da diyyar irin wadannan mutane da ba ta taka kara ta karya ba, don daurarrun su shaki iskar ’yanci.

“Yin hakan zai kawo saukin cunkoso a gidajen yari,” inji Biri.

Daga nan sai ya gargadi wadanda aka ’yanta din da su ji tsoron Allah su kauce wa aikin da zai maido su gidan a nan gaba.

Wadanda aka ’yanta din sun hada da Musulumai da Kiristoci don kara hadin kai a tsakanin bangarorin biyu.

’Yantattun fursunonin sun gode wa lauyan, sannan suka yi alkawarin kiyayewa, tare da yin kira ga sauran al’umma da su yi koyi da irin halin lauyan wajen ’yanta mazauna gidan yarin.