✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shari’ar batanci: Lauyoyin Sheikh Abduljabbar sun janye

Ci gaba da shari'ar bayan an kai malamin asibitin kwakwalwa.

Lauyoyin da ke kare Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara sun janye daga ba shi kariya a shari’ar masa bisa zargin yin batanci ga Manzon Allah (SAW).

Lauyoyin karkashin jagorancin Barista Haruna Magashi sun sanar da janyewarsu daga shari’ar ce a zaman kotun na ranar Alhamis da ya gudana a Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Jihar Kano.

Lauyoyin sun shaida wa kotun cewa sun janye daga shari’ar ne don radin kansu inda suka nemi kotun ta ba malamin damar daukar duk matakin da yake so wajen kare kansa.

An ci gaba da shari’ar malamin ne bayan kotun a zamanta na baya ta bukaci a kai shi asibiti domin duba lafiyar kwakwalwarsa da kuma jinsa, bayan ya ki cewa komai a zaman na wancan lokaci.

Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da malamin ne kan zargin da take masa na yin batanci ga Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SAW) sun janye daga shari’ar.

Bayan janyewar lauyoyin daga kare Abduljabbar Kabara, ya nemi kotu ta sahale masa kawo wasu lauyoyin da za su ci gaba da kare shi a shari’ar.

Alkalin kotun Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya amince da bukatar malamin, ya kuma dage sauraren shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Satumbar, 2021.

  1. Kwakwalwar Abduljabbar lafiya lau

Tun da farko kotun ta karbi sakamakon gwajin kwakwalwa da na kunne da ta sa a yi wa malmin daga Asibitin Kwararu na Murtala Mohammed da kuma Asibitin Masu tabin Kwakwalwa na Dawanau, inda sakamakon gwaje-gwajen guda biyu suka nuna malamin yana cikin koshin lafiya.

Idan za a iya tunawa a ranar 2 ga watan Satumba, kotun ta bayar da umarnin gwada lafiyar kwakwalwa da kunnen Sheikh Abduljabbar Kabara saboda kin amsa tamboayoyin da ta yi masa a yayin da aka karanta masa sabuwar takardar tuhumar da lauyoyin gwamnati suka gabatarwa kotun.