✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Larry King: Fitaccen dan jarida na asibiti bayan kamuwa da COVID-19

Sama da makonsa guda a asibiti ba a bari ’ya’yansa su ziyarce shi.

An kwantar da Larry King, shahararen mai gabatar da shirin tattaunawa a gidan talabijin na CNN a asibiti bayan ya kamu da cutar COVID-19.

Makusantan iyalan dattijon mai shekara 87 wanda ya shekara 25 yana gabatar da shirin Larry King Live a tashar CNN sun ce ya yi sama da mako guda a kwance a asibiti.

CNN ta ce saboda wasu dokoki, asibitin Cedar Sinai da ke birnin Los Angelis inda aka kwantar da Larry King ba su bari ’ya’yansa sun ziyarce shi ba.

Kafin kamuwarsa da COVID-19, Mista King ya dade yana fama da nau’i na biyu na cutar Suga da ciwon zuciya wadda ta sa sau hudu ana yi masa tiyata tun a 1987.

A 2017 ya sanar da kamuwarsa da cutar kansar huhu wadda aka yi masa tiyata; an kuma yi masa wata tiyatar lokacin da ya yi fama da ciwon zuciya a 2019.

Cutar da yake fama da ita ta sa ya kafa gidauniyarsa ta “Larry King Cardiac Foundation,” domin ba marasa inshorar lafiya damar kula da lafiyarsu.

Ya gabatar wa CNN shirin Larry King Live akalla sau 6,000 inda yake tattaunawa da ‘yan takarar shugaban kasa, taurarin fina-finai, ‘yan wasa, mashahuran mutane da sauran jama’a.

A shekarar 2010 ya yi ritaya daga aiki a CNN bayan ya shafe shekara 25 sai dai ba a jima ba ya sake dawowa fagen aikin jarida.

A 2012 ya fara gabatar da shirin “Larry King Now,” a Ora TV, wata tashar talabijin ta intanet da suka kafa tare da Carlo Sim, wani attajiri a harkar sadarwa dan kasar Mexico.

A 2020 manyan ’ya’yan Larry King biyu suka rasu cikin mako guda: Babban dansa, Andy King mai shekara 65 ya rasu sakamakon bugun zuciya a watan Yuli.

A watan Agusta kuma kanwarsa, Chaia King ta rasu bayan likitoci sun gano cewa tana fama da cutar kansar huhu.