An sallami Shugaban babbar kafar yada labarai ta CNN da ke kasar Amurka, Chris Licht daga aikinsa.
Shugaban Warner Bros. Discovery, kamfanin da ke mallakar CNN, David Zaslav, ya sanar da sallamar Chris Licht ne kwana biyu bayan Licht ya shaida wa ma’aikata a lokacin taron editoci cewa zai yi duk abin da zai iya don samun yardar mutanen da ke kusa da shi.
Zaslav ya sanar da sallamar Licht ne daidai lokacin da CNN ke fama da raguwar masu kallo da kudaden shiga, ga kuma yawan kurakurai a cikin shirye-shiryen da kafar take gabatarwa.
Adadin mutum 494,000 da ke kallon CNN a lokaci manyan shirye-shiryensa a watan Afrilu, ya ragu da kashi 16 a wata Mayu.
Cibiyar kididdigar kasuwanci ta S&P Global Market Intelligence, ta ce ribar Dala biliyan 1.2 da CNN ta samu a 2020 ya ragu zuwa Dala miliyan 892 a 2022.
An ruwaito cewa yawan kurakuren da ake samu a shirye-shiryen CNN ke gabarwa a wa’adin jagorancin Chris Licht ya sanyaya gwiwar ma’aikata.
Da yake sanar da sallamar Licht, Zaslav ya amsa wasu laifin wasu daga cikin matsalolin da kafar ta samu a bara.
Daga nan ya sanar da nada kwamitin shugabancin riko mai mu hudu, inda ya shaida wa ma’aikata cewa ana neman wanda zai maye gurbin Licht.
A lokacin da ka dauke shi aiki kimanin shekara guda baya, an dora wa Chris Licht alhakin inganta labaran CNN domin samun karbuwa ga duk bangaorin siyasar kasar Amurka.