Larabgana, ɗaya ce daga cikin daɗaɗɗun al’adun Bahaushe tun bayan zuwan addinin Musulunci. A al’adance, ranar na zuwa ne a kowacce Larabar karshe ta watan Safar (wata na biyu a shekarar Musulunci).
Ana alaƙanta ranar da munanan abubuwa da dama, sannan an bayyana abubuwa masu yawa da ake yi da waɗanda ba a yi a ranar, don kaucewa haɗuwa da wasu bala’o’i.
Sai dai bisa ga dukkan alamu, ƙaruwar ilimin addinin Musulunci ya ɗan dakushe kaifin ranar da wasu daga cikin al’adun da ake yi a cikinta.
Asalinta
A cewa Nasir Wada Khalil, wani masani kuma mai bincike kan al’adun Hausawa da ke Kano, akwai tarin abubuwan da ake yi a ranar.
Ya ce, “Da farko dai ma ita kanta ranar an fara ta ne tun bayan zuwan Musulunci ƙasar Hausa. Ana alaƙanta ta da munanan abubuwa masu yawa. Ana ma ganin a ranar ce Abrahata ya kai hari da nufin rushe ɗakin Ka’aba da ke birnin Makkah, har Allah Ya aiko masa da tsuntsaye suka tarwatsa shi da tawagarsa.
“Sannan a al’adance, Bahaushe na ganin a ranar ce ake saukar da duk wani bala’i na shekarar. Don idan ba a yanzu ba, a baya Bahaushe ko aure ba ya yarda ya ɗaura gaba ɗaya a watan, saboda kauce wa bala’o’in,” in ji shi.
Abubuwan da ake yi a ranar
A cewar masanin, akwai al’adu da yawa da ake yi a ranar.
“Daga cikinsu akwai rubuta ayoyin nan na “Salamun-Salamun” na cikin Alƙur’ani a allo a wanke sha domin neman tsari. Wasu ma na cewa sai an debo ruwan rijiya bakwai a sha, amma dai wannan ba dole ba ne. Idan ma aka samu na famfo ko na roba shi ma zai yi.
“Kazalika, a kan samu farar albasa a saka a cikin rubutun, duk domin neman tsari. Ko a gargajiyance kuma dama ai albasa dafa’i ce daga cututtuka kamar su sanyi.
“Idan an rubuta, ana ƙara ruwa a ciki ana wankewa ana ba mutane da makwabta su sha. Manya da yara, maza da mata da tsofaffi kowa yana sha domin neman kariya.
“Sannan akan bayar da shawarar mutane su kiyayi barin kayan amfanin gida a bude, sannan ba a fitowa da daren ranar, ko fitsari mutum yake ji sai dai ya tafi da mazubi ya yi a ciki, alabasshi da safe ya zubar.
“Sannan da daddare akan zauna a yi sallah, ya danganta da adadin da mutum zai yi, daga raka’a hudu dai zuwa sama, don neman tsari daga masibun wannan shekarar.
“Bugu da kari, ana so a bar kwanuka da mazubai a rufe, a wannan daren. Amma a kodayaushe ma ana so mutum ya saba da irin wannan al’adar saboda gudun munanan kwari da dabbobi irin su tsaka kada su rika shiga ciki,” in ji Nasir Khalil.
Masanin ya ce da yawa daga cikin abubuwan suna da asali a addinin Musulunci, kodayake ya ce wasu suna wuce gona da iri.
“Misali, wasu za ka ji ko wanka ba sa yi a ranar, sannan wasu sam ba sa ɗaura aure a cikinta. Sannan shi kansa ruwan wanke rubutun ai ka ga wasu cewa suka yi a haɗa da ruwan rijiya bakwai, amma duk waɗannan ba su da asali.”
‘Tasirin addini ya disashe wasu al’adun ranar’
Nasir Khalil ya kuma ce tasirin ilimin addinin Musulunci ya taimaka wajen daƙile wasu daga cikin al’adun da ake a ranar, inda malamai ke ganin yawancinsu ba su da asali.
Ya ce, “Shi kansa rubutun sha alal misali, ai ka ga wasu ma ƙyamar shi suke yi, makarantun ma yanzu ai na tsangaya da na allo sun ragu, an koma na zamani masu amfani da biro da takarda a maimakon tawada da alƙalami.
“Amma duk da haka, a yanzu ana samun mutane na yin mi’ara-koma-baya, saboda hatta waɗanda a baya suke ƙyamar shan rubutun a yanzu sun dawo suna sha,” in ji shi.
Al’adar ba ta da asali a Musulunci – Malamin addini
Dokta Abdullahi Muhammad, limamin masallacin Juma’a na unguwar Hotoro da ke Kano ya ce wannan al’ada ba ta da tushe ballantana makama a addinance, hasalima ma bidi’a ce, in ji shi.
Ya ce, “Wata ko dare ko wuni daya ne daga cikin abubuwan da Allah ne ke tsara su. Dukkansu ba su da tasiri wajen ƙaddara wani abu na kyau ko ko akasin haka. Halittu ne na Allah da ke gudana kamar yadda Ya halicci komai.
“Amma lokacin Jahiliyya sai mutane suke kallonsa [Safar] da watan da bala’i ke sauka. Amma yanzu bayan zuwan Musulunci malamai sun kore su domin akwai abubuwan da addinin ya tsara a yi idan an fuskanci bala’i ko an ga yana tunkarowa. Ita kuma waccan al’ada ba ta tabbata ba cikin Alƙur’ani ko sunnar Manzon Allah (SAW) ko Sahabbansa ba.
“Malamai sun tabbatar bidi’a ce ba ta da asali ba ta da tushe. Hasalima kudircewa ka ce watarana guda daya bala’i na sauka ya saba wa tsarin addinin Musulunci,” in ji limamin.