✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta kwace kujerun ’yan majalisar PDP 4 a Filato

Sai dai jam'iyyar PDP a jihar ta ki amincewa da hukuncin da kotun ta yanke.

Kotun sauraren kararrakin zabe ta ’yan majalisun tarayya da na jihohi da ke zamanta a Jos, ta soke zaben ’yan majalisar dokoki hudu na Jam’iyyar PDP a jihar.

Da yake karanta hukuncin kwamitin alkalai guda uku, Mai Shari’a Mohammed Tukur, ya sanar cewa ’yan takarar PDP a jihar ba su da inganci, saboda jam’iyyar ba ta da shguabanci a jihar.

’Yan majalisar da kotun ta soke zabensu su ne Peter Gyendeng mai wakiltar mazabar Barkin-Ladi/Riyom tarayya; Musa Bagos mai wakiltar mazabar Jos ta kudu/Jos ta gabas; Beni Lar mai wakiltar Langtang ta Arewa/Langtang ta Kudu Mazabar Tarayya da kuma Napoleon Bali mai wakiltar Filato ta Kudu.

Wadanda suka ci gajiyar hukuncin kotun sun hada da Fom Dalyop da Ajang Alfred Iliya na jam’iyyar Labour Party mai wakiltar mazabar tarayya ta Barkin-Ladi/Riyom da Jos ta Kudu/Jos ta Arewa;

Vincent Bulus Venman na jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Langtang ta Arewa/Langtang ta Kudu da kuma Simon Lalong mai wakiltar mazabar Filato ta Kudu.

Jam’iyyar PDP a jihar ta yi watsi da hukuncin kotun, wanda ta ce ya saba wa hukuncin da wata kotun sauraren kararrakin zaben ’yan majalisun tarayya ya yanke a baya.

Sai dai kuma, lauyoyin masu shigar da kara da wadanda ake kara sun ce sun yi na’am da hukuncin hukuncin da kotun ta yanke.