✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lampard ya fara da kafar hagu bayan dawowa Chelsea

An nada shi kociyan rikon kwarya zuwa karshen kakar nan a makon nan.

Frank Lampard ya ce baya jin za a magance matsalar Chelsea a rana daya, bayan da ya fara da kafar hagu a Wolverhampton.

Lampard wanda ya ja ragamar Chelsea a karon farko a matakin rikon kwarya, ya yi rashin nasara 1-0 a gidan Wolves a wasan mako na 30 na Firimiyar Ingila ranar Asabar.

Wasan farko da ya shugabancin Chelsea tun bayan wata 27 da aka kore shi a Stamford Bridge, Thomas Tuchel ya maye gurbinsa.

Chelsea ta kasa zura kwallo a raga a wasa uku a jere kenan, karo na 11 da aka doke ta a babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.

”Aiki ne babba a gaba, in ji Lampard, wanda Chelsea ke mataki na 11 a teburin Premier League.

”Mun kwan da sani ba ma yanayi mai kyau, ba wanda muke bukata bane, amma da akwai dalilin hakan.”

”Ban jin zan warware matsalar nan a kwana daya, dole sai mun kara kwazo a wasa da sa kaimi.”

Wasa hudu kenan da Chelsea ba ta yi nasara ba, wadda a mako mai zuwa za ta je gidan Real Madrid, domin buga Champions League.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Chelsea a wasan farko a quarter finals a babbar gasar zakarun Turai ta kakar nan.

Lampard, wanda bai da kungiya tun bayan da Everton ta sallame shi a Janairun 2023, ya horar da Chelsea daga Yulin 2019 zuwa Janairun 2021 daga nan ta kore shi.

An nada shi kociyan rikon kwarya zuwa karshen kakar nan a makon nan, bayan da Chelsea ta kori Graham Potter ranar Lahadi, wanda ya yi wata bakwai.

Tun farko Chelsea ta sa Potter ya yi murabus daga aikin Brighton, sannan ta kulla yarjejeniyar shekara biyar da shi.

Lampard ya buga wa Chelsea tamaula a Stamford Bridge lokacin da Roberto di Matteo ya ja ragamar kungiyar ta lashe Champions League a 2012 a matakin rikon kwarya daga baya aka bashi jan ragama.