Kocin Bayern Munich, Thomas Tuchel, zai bar kungiyar a karshen wannan kakar wasannin shekara ɗaya kafin kwantiraginsa ya ƙare.
Bayanai sun ce zai raba gari da ƙungiyar ne sakamakon kashi da ta sha sau uku a jere, lamarin da ya sa ake hasashen cewa za ta ƙare kakar bana ba tare da ɗaukar kofi ko ɗaya ba.
- Ba gudu ba ja da baya kan zanga-zangar gama-gari da za mu gudanar — NLC
- Tinubu ya naɗa Kemi Nanna Nandap shugabar hukumar shige da fice
Bayern ta ce an yanke shawarar sallamar Tuchel ne bayan ya tattauna da shugaban ƙungiyar Jan-Christian Dreesen dangane da sauye-sauyen da take yi.
“A tattaunawar ƙeƙe-da-ƙeƙe da aka yi, mun yanke shawarar kawo ƙarshen alaƙarmu ta aiki a bazara bisa yarjejeniyar da duka ɓangarorin muka amince da ita,” a cewar wata sanarwar da ƙungiyar ta ambato Dreesen yana bayyanawa.
“Babban burinmu shi ne mu samu sabon tsarin ƙwallon ƙafa wanda sabon koci zai jagoranta a kakar 2024-25.”
Tuchel ne ya jagoranci Bayern a nasarar lashe kofin Bundesliga a kakar bara bayan ya karɓi ragarmar gudanar da ita a bazara, amma a halin yanzu ƙungiyar tana bayan Bayern Leverkusen da tazarar maki takwas.
Ɗaya daga cikin wasannin ne inda Leverkusen ta doke ta da ci uku da nema – kuma Lazio ta doke Bayern Munich da ci ɗaya da nema a wasansu na farko a zagaye na sili-ɗaya-ƙwale na zagayen ’yan 16 a gasar Zakarun Turai.
Tsohon kociyan na Chelsea mai shekaru 50 ya maye gurbin Julian Nagelsmann ne a watan Maris din 2023, inda ya ƙulla yarjejeniyar har zuwa watan Yunin 2025.