✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lambar yabon da Saudiyya ta ba ni ta sa ni kuka -Sheikh Lemu

Kwanan nan kasar Saudiyya ta ba babban malamin addinin musukluncin nan Sheikh Ahmad Lemu, shugaban Cibiyar yada addinin musulunci da ke Minna jihar Neja, lambar…

Kwanan nan kasar Saudiyya ta ba babban malamin addinin musukluncin nan Sheikh Ahmad Lemu, shugaban Cibiyar yada addinin musulunci da ke Minna jihar Neja, lambar yabo ta Sarki Faisai, domin yabawa da gudunmawar da yake bayarwa wajen cigaban addinin musulunci. Wanda ya sanya ya zama dan Najeriya na biyu da ya taba samun lambar yabon, baya ga marigayi Sheikh Abubakar Gumi, wanda shi ne dan Najeriya na farko da ya samu. Aminiya ta tattauna da shi inda ya yi bayani game da karramawar da aka yi masa da kuma sauran al’amura da suka shafi kasa, kamar haka:

 

Aminiya: Akramukallah,ya ya ka ji ne da aka ce ka cancanci samun wannan lambar yabo ta Sarki Faisal?
Sheikh Ahmad Lemu:To gaskiya kuka na yi. Idan dai gaskiya kake so. Daga ni sai ita mai dakina, ita Baturiyar, sai Allah.Waya aka yi wo mini, na je wajen gidanmu don in amsa, sai gashi ana gaya mini cewa ina yi maka barka game da wannan lambar yabon . daya daga cikin abokanmu da ke can Saudiyya ne ya sanar da ni, da muka gama na shigo cikin gida domin in shaida wa matata A’isha labarin, sai na fashe da kuka.Sai ta tambaye ni, me ya sa ka kuka? Na shaida mata, sai ta ce, ai maganar farin ciki ce. Sai na ce mata a’a, ba da wannan idon ni ke dubar ta ba. Akwai ayoyi guda biyu na karshen Suratul An’am, wato Sura ta 6 a cikin Al-Kur’ani Mai girma,abin da Allah Ya fada a ayoyi biyun nan shi ya sa ni kuka.Ta ce,tana son in karanta mata.Sai na lura cewa tunda ni ke ban taba samun wani abun da za a kira na daraja da ya kai wannan ba. In lambar yabo ce ta farko wanda Janar Abdul-Salami ya ba ni OON, a’a ta sama da ita ce OFR wanda Obasanjo ya ba ni, duk wadannan wanda Bature ke ce wa ‘National Honour’ na kasa ne, duk bai wuce kasar Nijeriya ba .Haka nan wadansu lambobin yabon da na yi ta samu na digirin girmamawa daga Jami’ar Usmanu dan Fodiyo, ko na Jami’ar Fountain ko na,Jami’ar Crescent,ko na kasar  Kuwait ne da sauransu, a wuri na wannan ta marigayi Sarki Faisal din ta fi daraja. Sai na dauka cewa a halin yanzu na zama tamkar wanda yake zaune ne a dakin rubuta jarabawa, a ce duk wadanda aka ba ka a baya ka ajiye su a gefe, ga wadda ta fi kowacce nan an ba ka na duniya baki daya.Tamkar gwaji ne daga Allah domin Ya ga abin da zan yi bayan  wannan lambar yabon da aka ce na cancanci a ba ni,wannan shi ya sani hawaye. Ita mai dakina tana ta ba ni hakuri da duk maganar da za ta kwantar mini da hankali.Wannan lambar yabon ta kashe mini jiki.Idan na tuna wadannan ayoyin, in kasa murna, in ba kamar yadda ka nema ba. Yadda na ji ke nan.
Aminiya:Ka dade kana gudanar da wa’azi da da’awa, ka taba sa ran samun irin wannan lambar yabon?
Sheikh Ahmad Lemu:Ina fa? ko ta kasar da aka ba ni, wane ni? Wato al’amari ne daga Allah. A kan wannan na tsaya, har ta kai ga tsohon shugaban kasa Janar Abdul-Salami Alhaji Abubakar ya ba ni lambar yabo ta farko a rayuwata ta OON. Idan an ce ai shi musulmi ne,tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo fa,wanda ya ba ni wadda ta fi waccan daraja, wato ta OFR. Babu wata hanyar da mutum zai yi tunanin haka.Ka ga ba ni kadai ke aikin da’awa ba,kuma ban fi kowa iyawa ba.Duk da cewa ita Cibiyar yada addinin musulunci (I.E.T) muhimmin aikin da ta sa a gaba shi ne yada addinin Islama, ba a Nijeriya ba, har zuwa kasashen waje, da suka hada da Sudan da Bahrain da Malesiya da Ostireliya da Sri Lanka. Kafin in manta, a nahiyar Afrika muna ayyuka a kasashen Saliyo da Liberiya da Kamaru, muna tura mutanenmu domin gudanar da ayyukan da’awa.Wadannan na daga cikin ayyukan da na tashi tsaye domin ganin mun cigaba da aiwatar da su.
Ba mu tsaya a nan ba, mun shiga gudanar da bincken da ya kai ga buga littattafai da mukaloli wanda muke da cibiya guda wadda ke da alhakin haka, wato Cibiyar Kula da Ayyukan Da’awa.Wannan cibiyar tana koya wa jama’a dabarun da za su bi wurin gudanar da ayyukansu ta hanyar zaman lafiya ta amfani da hikima ga wadanda ba musulmi ba. Mun karanci wadansu abubuwa game da addinin Kirista.Duk wanda ya karanta littafina wanda na wallafa da harshen turanci mai suna’MORALITY IN ISLAM’,zai ga duk abin da na fada a ciki,da abin da ke tsakaninmu da mabiya addinin Kirista,da addinin Kiristancin da sauransu.Akwai mutane da yawa wadanda su ma suna irin wadannan ayyukan namu.Ban raina ayyukan da muke yi ba, kuma ko kadanbai ba ni mamaki ba.kasar Kuwait ta taba gayyata ta taro suka ba ni lambar yabo.
Aminiya:Mene ne kake tunanin kara yi domin bunkasa musulunci da musulmai?
Sheikh Ahmad Lemu:Tun daga lokacin da Shugaba Goodluck Jonathan ya nada ni Shugaban Kwamitin Binciken Tarzomar Bayan Zaben Shekarar 2011,da suka kai ga tashin hankalin da suka hada da kone-kone.Wannan aikin da na yi,na tuna na dauki wani mataki.Na gaya wa membobin Kwamitinmu cewa,akwai wadansu ‘Yan Arewa wadanda idan ka tashi maganar neman gaskiya tsakaninka da su,idan ba tsakaninka da Allah da shi wanda kake magana da shi ba,ba za su bude maka cikinsu ka san gaskiyar al’amari ba. Ba shakka,na ce wa kwamiti dina, akwai wadanda ba sai na gaya muku sunansu ba,wadanda daga ni sai su sai Allah, don in ji gaskiyar al’amari, haka kuwa ya faru. Na ce zan kawo muku duk abin da na tsinta a wurinsu,ba zan gaya muku ga abin da wane kaza ya gaya mini ba. Haka na yi da wadansu manya-manyan Sarakuna da wadansu gwamnoni,da wadansu tsofaffin shugabannin kasar nan.Haka kuwa suka bude mini gaskiya tsakani da Allah.Shi ya sa rahotonmu ya samu karbuwa a duk kasar.Me ya hana gwamnati amfani da shawarwarin da ke kunshe a rahoton,ni na dauka kila lokaci ne bai yi ba. Ni dai ina daukar kaina talaka ne wanda aka nemi in yi aikin da Shugaban kasa ya sa ni,kuma na yi tsakanina da Allah. Sanadiyyar wannan aikin da na yi,na gano wadansu abubuwa dangane da kasar nan,wadanda suka shafi wannan tambayar da ka yi mini.
Daga wancan aikin da na shugabanta zuwa na kwanan nan, watau na sasantawa da ‘Yan Boko Haram, da Minista Kabiru Tanimu Turaki ya Shugabanta,na gane cewa abubuwan da ke jawo tashin hankali a kasar nan ‘Yan Siyasa ne da Malamai da sauransu,son zuciya ne suka sa a gaba.Mutum ya dauka a ransa ga abin da nike son a yi, ko ga abin da ban so a yi,ba tare da la’akari da alheri ko akasin da ke tattare da haka ba,daya ke nan.Sai tara kazamar dukiya na takardun naira da dala.Da son mulki da mabiya.Wadannan abubuwa guda uku,sun ci ran mutane da yawa a kasar nan.Bugu da kari,muka lura kuma wajen neman wadannan abubuwan guda uku,babu tsoron Allah,balle kunyar dan Adam.Yayin cim ma wannan burin da aka sa an daina tsoron Allah da na tashin al-kiyama da rashin kunyar  dan Adam, an dauka duk wanda zai shiga gabansu domin kar su cimma burinsu, sai a kashe shi,ba a kuma damu da ko rayuka nawa za a rasa a sakamakon wannan ran da za a rasa ba. Abubuwan da suka addabe mu dangane da al’amuran kasar nan ke nan. Sai muka komo a nan cibiyar I.E.T muka yi nazarin matakin da ya kamata mu dauka domin cusa wa jama’a dabi’u nagari.Wannan ne ya sa a matakin farko muka bullo da wani shiri da muka yi wa lakabi da ‘ETHICAL REFORM PROGRAMME’.Sai mataki na biyu na TRAINING THE TRAINER DIALOGUE IN ISLAM AND DA’AWA .Sannan na uku wanda muka yi wa lakabi da GRASSROOT PROGRAMME, wato yadda za a yada addinin Islama da manufarsa a tsakanin jama’a baki daya, musamman wadanda ke yankunan karkara.Sai na hudu ISLAMIC PERSPECTIbES, wato al’amarin Ilimi da yadda za a yada shi a musulunce, da yadda za a fahimce shi a rayuwar jama’a. Na karshe shi ne yadda za mu yada wadannan al’amura a duniya baki daya. Mun ga nasarorin wadannan ayyukan da na sa a gaba, a ciki da wajen kasar nan. A kansu kuma nike kafin wa’adi ya cika.
Aminiya: Kwamitinka da na Kabiru Tanimu sun mika wa shugaban kasa rahoto amma ba a yi komai ba game da naka tukun,ya ya ka ji da wannan lamarin?
Sheikh Ahmad Lemu: Na farko dai ba ni ne shugaban kwamiti na sasantawa da ‘Yan Boko Haram ba, minista Kabiru Tanimu Turaki shi ne shugabanmu gaba daya.Ba shakka,ya nada shugaban wani karamin kwamiti, tare da shi ne muka yi aiki na haduwa da ‘Yan Boko Haram din ma.Ba aikina ni kadai ba ne,ban kuma san halin da gwamnati ke ciki ba.Tana da niyyar aiki da rahoton da muka mika musu,ban sani ba.Yadda na gaya maka,ayar nan dai ta Suratul An’am, duk abun da mutum ya aikata shi za a rubuta masa, ba wani ba. Da yake haka al’amarin yake da na zamanin da aka yi tarzomar zaben shekarar 2011, mun shaida masa gaskiya, amma mun ji shiru ba a aiwatar da komai ba,idan ma an aiwatar da wani abu to dan kadan ne. Duk da wadansu abubuwan da muka gaya masa zai yi wa gwamnatinsa da jam’iyyarsa da komai ya zama musu alheri.
Aminiya:Me za ka ce ga jama’a wadanda ke kafa kungiyoyin addini domin cim ma burin kansu?
Sheikh Ahmad Lemu:Wasunsu kam babu shakka domin cim ma burin kansu ne suke abubuwa. Ai na gaya maka cewa abun da ya addabe mu a kasar nan,son zuciya da son dukiya da son mulki hade da mabiya. Bari a dauki misali, kamar Izalah da darika,mece ce manufar Izalah,idan  ka dubi Al-kur’ani,abin da za su daura a baki shi ne,a samu wadansu daga cikinku wadanda za su yi umurni da a yi ayyukan alheri yadda Allah Yake so,sannan suna hani da mummunan ayyuka.Wa zai ce, wannan ce manufar ta saba wa Kitabu wa Sunnah,bai saba ba.Amma yaya  da yawa a cikinsu suke kira zuwa ga addinin musuluncin? Ya kan saba wa ayar da Allah ya ce,Ka yi kira zuwa ga hanyar Allah ta hanayar hikima da wa’azi mai kyau,kuma idan abun musu ne, to ku yi jayayya ta hanyar da ke da kyau. Amma Ka zo ka kafirta wannan, ka muzanta wancan, ka wulakanta wannan, ka yi wa wannan habaici,don ka samu cim ma burin abun da kake so,ganin cewa mutane da yawa ba su san ma’anar abin da Al-Kur’ani ke fadi ba,ka dauka kai ne Malami,ka canza ma’anar,ka fadi abin da ka ga dama.Yin haka ya saba wa Kitabu wa sunnah.
Me ‘Yan darika suke yi?Zikiri suke yi,suna girmama Ubangiji, suna kirarin Allah.Ko a masallacin Manzon Allah (SAW) akwai hadisin nan na Mu’awiya da ya zo a cikin RIYADUL SALIHIN na Sheikh Nawawi. Manzon Allah ya shigo cikin masallaci sai ya tarar da wadansu mutane a zazzaune suna zikiri,sai ya ce musu, na hada ku da Allah me ya sa kuke wannan? Sai suka ce masa muna neman kusanta ga Ubangiji da girmama shi ne ya sa muke haka. Sai ya tambaye su, kun san abin da ya sa na hada ku da Allah? Suka ce a’a, Allah  da mala’ikunsa ne kadai suka sani. Sai ya ce mala’ika Jibrilu ne ya zo ya ce mini in gaya muku Allah yana alfahari da ku a kan mala’ikunsa. Za a ce wannan aikin babu kyau? Saboda haka zikiri suke.Me Allah ke cewa game da zikiri, aya ce take umurnin a yi zikiri da safe da maraice,haka ‘Yan darika suke abunsu.Ga irin ladar da za su samu,Allah Ya bayyana .Wa zai ce ya saba wa sunnar Manzon Allah [ S.A.W]? Bai saba ba.Me ke faruwa?Sai ka ga wadansu Shugabannin zikirin su dauki kansu tamkar waliyyai ne,kamar su ke da gafarar da za a raba wa mutane.Wani idan ya fitar da kaki,wadansu su dauka su hadiye. Ashe ba wuridin ne illa ba,halayen da wadansu ke nunawa ta yadda ake mayar da su kamar gumaka shi ne illa. Idan kamar a yadda na kawo ayar da take magana kan kira zuwa ga hanyar Allah ta amfani da hikima,ba haka ‘Yan Izalah ke amfani da hikima wurin kawar da munanan bidi’a ba.

Cigaba a shafi na 3

Daga shafi na 2

Ya jawo hadisin Manzon Allah dukkan bid’a bata ce,dukkan bata kuma wuta ce.Sai ya fassara Hadisin a juye. Shehu Usmanu dan Fodiyo ya bayyana a daya daga cikin litattafansa da ke cewa ba kowace bid’a ce mummuna ba.Sai ya ce,akwai bidi’ar da take dole a yi don karfafa addini. A nan ya bayar da misali da Al-Kur’ani, ya nuna a zamanin Manzon Allah bai da digo da wasulla da shadda,da su dauri da yamala.Daga baya ne su Hajajju Bin Yusuf suka kago,bayan da musulunci ya shiga nahiyoyin da ba na Larabawa ba, don su iya karatun  da salo iri daya.Da kuma ba haka aka yi ba karatun zai zo da sabani da yawa. Idan kana maganar abin da Manzon Allah bai yi ba,shi ne bidi’a, ga wannan yana zama tilas a aikata shi.Ya ya za ka yi da shi? A wannan littafin ya bayar da misalan bidi’a muharrama,ya kuma bayar da wajiba,ya kuma bayar da su daki-daki.Wadansu na bayar da misali da marigayi Sheikh Mahmud Gumi,ya rubuta littafi mai suna KITABU WURDIL  AZIM,ni ma ina da shi.Me ya fada a ciki,ga wannan wuridin,ga yadda Manzon Allah ya ce a yi.Ga istigifari, ga yadda ya kamata a yi.Ga salatin Annabi,ga yadda ya kamata a yi. Zikirin da ‘Yan darika suke yi daga wurin shaidan ne? Ai shi ne tushen Izala a Najeriya,ko ba shi ba ne?Daga baya wadansu mabiyan suka wuce gona da iri.Ba su tsaya a inda shi ya tsaya ba.Saboda haka ni a ra’ayina a ce za a kafirta mutum,yaushe mai Kalmar la’ilaha ilallah ya zama kafiri? Manzon Allah ya ce,idan ka ga musulmi ya kira dan uwansa musulmi kafiri,alhali ba haka abun yake a wurin Allah ba,zargi,ko kagen kafircin nan ya koma kan wanda ya yi shi. Akwai hadisin Manzon Allah da ke cewa, idan ka yi wa mutum kage da kafirci da fasikanci da munafunci,alhali ba haka mutumin yake a idon Allah ba,kai ne kafirin,ko munafikin,ko fasikin.Yaya za ka yi da wannan? Ka tsaga zuciyar mutum ne ka tabbatar da haka yake?Duk irin wadannan zarge-zargen sun saba wa KITABU WA SUNNAH wajen fahimta.Saboda haka ba daidai ba ne.
Aminiya: Matsalar bambancin addini ta kunno kai sosai a kasar nan,ta yaya kake ganin za a rage kaifin wannan matsalar kafin zaben shekarar 2015?
Sheikh Ahmad Lemu: Ai ba ma addini kawai ba ne.Duk rigingimun duniyar nan abun da Bature yake cewa ‘DIALOGUE’wato a tattaunawa cikin fahimta.Ga nawa ra’ayin,gaya mini naka ra’ayin. Idan aka samu fahimtar juna shi ke nan. Ci naka in ci nawa ba rowa ba ne.Ita ce.Sannan kowa ya fahimtar da jama’arsa ta hanyar KITABU WA SUNNAH.Tsakani da Allah, ku musulmi ku fahimtar da jama’a ga yadda yake a Al-Kur’ani,ba fassarar zuciya ba.Ga abin da Allah yake nufi,kuma kai ga yadda ka fassara don a bi ra’ayinka,kai ne Malami,ko kai ke da gaskiya. A ji tsoron Allah,a ji kunyar Manzon Allah [S.A.W].Haka ma tsakaninmu da Kiristoci,mu fada musu yadda al’amarin yake. Akwai wata rana game da irin wannan tambayar da aka yi mini a inda muke horo da tarbiyyar ma’aikatanmu.Shi ke nan,muka ce ga abubuwan da ke tsakaninmu da ku haka Annabi Isah [AS] ya ce,haka Annabi Muhammad [S.A.W] ya ce.Aka fito da su daya bayan daya.Sai aka wayi gari ya bayyana a littafinsu na Bibul da shafuka,da komai. A fahimtar da juna,amma  idan aka zo ana zagin juna yadda wadansu Shugabannin Addinin Islama da na Kirista ke yi,kiyayya ba za ta kare ba.
Aminiya:Daga cikin ‘Ya’yanka akwai wadanda suka fara bin hanyarka ta wa’azi da Da’awa?
Sheikh Ahmad Lemu: Akwai su maza da mata,ko shakka babu.Idan ka yi maganar bin sawu sosai akwai namiji wanda tunda ya gama ilimin jami’a,bai yi aikin komai ba sai na wannan kungiyar.kanwarsa ma haka take.Na gode wa Allah.Sauran ma suna aiki da gwargwadon tarbiyyar da muka yi musu.Ka ga wadansu abubuwan,tare muke yi.
Aminiya:Kwanan nan Shugaba Goodluck Jonathan ya sa wa dokar haramta auren jinsi daya hannu, inda aka tanadi hukuncin shekru 14 ga duk wadanda aka kama suna aikata haka,ka gamsu da hukuncin?
Sheikh Ahmad Lemu:Ni ban karanta dokar daga farko har karshe ba.Ma’anar dokar dai a kataice an hana aure tsakanin jinsi daya,kamar mace da mace,namiji da namiji,ma’ana aikata luwadi.Ba yadda za a yi mutum ya halalta abin da Allah Ya haramta a zauna lafiya.Irin wadannan abubuwan ne ke jawo wa mutane bala’i.Ta haka ne kuma Allah Ya fifita dan Adam a kan kowace halittar da ya halitta.Sai muka zo a wajen aiki,bayan da tun daga farkon dan Adam cewa ya yi zan sa halifana a bayan kasa,har Mala’iku suka ce,za ka yi abu kaza da kaza.Ya ce ni na san abun da ba ku sani ba.Har aka samar da Annabi Adam [A.S] a matsayin halifan Ubangiji,da ‘Ya’yansa.Sai a yanzu ne za mu ce mu za mu halalta abun da ko dabbobi ba su aikatawa. Misali,kare namiji ba zai barbari kare namiji dan uwansa ba,sai dai su yi tsiya suna cizon juna a kan karya.Haka ma kaji da tsuntsaye ba su aikata irin wannan hali na abin takaici.A ce dan Adam ya kaskantar da kansa wurin aikata abin da ko birai ba za su aikata ba.Sai in ce tabarakallah.Mun jinjina masa.Allah Ya saka masa da alheri.
Aminiya: Sa wa dokar nan hannu ya sa kasahen yamma suna yi wa Najeriya barazana,Me za ka ce game da wannan barazanar?
Sheikh Ahmad Lemu: Idan dai muna da ‘yancin kanmu da muke mulkin kasar nan bisa tsarinmu.Ina ruwansu da abun da muka ga shi ne daidai ,idan sun zama karnuka ko kuma birai game da yadda suke gudanar da rayuwarsu,wai su suna martaba ‘yancin ‘’Yan Adam, su je su yi ta binsu.Kowa zai gamu da Allah gobe lahira.Mu da muka ce ba za mu yi ba, duk dai wuri daya za mu.Idan mun je zai yi hukunci,Ya kuma nuna musu cewa su ne suka saba wa ka’idarSa .Ubangiji Ya hana zina tsakanini mace da namiji,me za ka ce na tsakanin mace,da mace.Da me suke wannan tsiyar?Ai da ma kunya.Ina ruwanmu da su? Su kira mu duk abin da suka ga dama. Allah Ya fada mana a Al-Kur’ani cewa za mu ji zancen banza daga wurinsu babu iyaka,da kuma wadanda suke maguzawa.Musulmi ne suka fi yawa a Najeriya gaba daya. Idan muka yi hakuri,muka ji tsoron Allah,shi ke nan.
Aminiya: Dattawan Arewa na kokarin maka tshon Babban Hafsan Sojojin Najeriya Laftanar Janar Azubuike Ihejirika Kotun Duniya da ke birnin Hague,saboda barnar da sojoji suka yi a birnin Bama ta Jihar Borno,Me za ka ce game da haka?
Sheikh Ahmad:Tunda ni ba ni da cikakken bayani game da abubuwan da suka faru, idan daga kotun ne gaskiya za ta fito,da yake an taru an yi masa wannan zargin ya je ya kubutar da kansa mana.Idan gwamnati ce za ta goyi bayansa,sai su je su  gamsar da kotun duniya cewa ba laifinsa ba ne.Abu ne da ya faru kowa ya gani.barnar da sojoji suka yi,an gani.Wadanda aka yi abun a kan idanunsu suna nan.Wadansu an kashe su,wadansu suna raye.A je kotun mana,kotun ta tantance komai a fito da gakiya. Idan yana da gaskiya,ko bai da gaskiya,ta gaya wa duniya.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga Malamai da Musulmai da ‘Yan Najeriya?
Sheikh Ahmad Lemu: Na farko ga Malamai.A yi kokarin ilmantar da jama’a a hankali ta amfani da hikima da wa’azi mai kyau.Wato fahimtar da su tsantsar abun da ruhin musulunci yake na abin da Allah Yake koyarwa.Wannan ya hada da dabi’u da halaye da magana gwargwadon iyawa. A san yadda za a yi hani na dukkan abun da aka san ya saba wa tafarkin Allah da ManzonSa. A yawaita ayyukan da za su dasa tsoron Allah a zukatan jama’a.Duk wadannan ayyukan na Malamai ne.Su kansu su zama abun koyi.Ba abin da suke fadi daban,abin da suke aiwatar wa daban ba.
Musulmai kuma,kowa ya dukufa ya nemi ilimi da ittifakin zan koma wa Mahaliccina a kowane lokaci. Ko Malami bai taso ya yi magana ba, kai ka je ka nema.Gwargwadon abin da ka ji kuma ka yi aiki da shi.Wanda yake na hani,ka hanu,wanda yake na yi,a yunkura a yi. Nafilolin da Manzon Allah ya karfafa yin su irin azumin Litinin da na Alhamis,wadanda za su kara kusantar da kai zuwa ga Allah,ka yi.Haka ma sallolin tahajjud da na dare da sauransu a rungume su. A tuna da dukiya da mulki da son duk wani abu na kawa a nan duniya za a bar shi. Daga lokacin da ka mutu,zuwa lokacin da za a tayar da kai, komai dadewa za ka ce kamar ba ka yi zaman duniya ba.Kwatankwacin wanda ya yi barci daga safiya zuwa lokacin walha.Baki daya karshen maganar,daga wuta ce sai aljannah. Masu sace-sacen dukiyar nan idan ka bincike su daya bayan daya za ka gane cewa suna cikin firgita ne,babu wanda yake da kwanciyar hankali.Lokacin da nike dalibi a Landan an taba yi wa Paul Gate tambaya,a lokacin shi ya fi kowa arziki a duniya,sai da aka gama masa tambayoyi a talabijin ina kallo,aka ce masa,are you happy? ya ce no?’ Ina amfanin dukiyar da ka mallaki dukiya mai yawa amma babu kwanciyar hankali?
Ga ‘YanNajeriya kuwa,duk kiran daya ce. A koma ga Allah.Da Musulmai da Kiristoci game da halayenmu da ayyukanmu  baki daya.