✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lambar NIN: Za a yi wa ’yan Najeriya da ke Amurka rajista

Nan gaba kadan za a fara yi musu rajistar shaidar katin.

Za a yi wa ’yan Najeriya mazauna Amurka rajistar lambar shaidar dan kasa (NIN).

Karamin Ofishin Jakadancin Najeriya da ke New York ya shaida wa wani zama da ya yi da ’yan Najeriya a birnin cewa ya kusa kammala shirye-shiryen fara yi musu rajistar shaidar dan kasar.

Jakadan Najeriya a birnin, Lot Egopija ya shaida wa taron cewa bayan samun umarni daga Ma’aikatar Sadarwa ta Najeriya, ofishinsa ya fara aiki da Hukumar Kula da Shaidar ’Yan Kasa (NIMC) gabanin fara rajistar.

A cewarsa, ofishin ya kara inganta ayyukansa ga ’yan Najeriya mazauna Amurka a bangaren bayar da takardun fasfo da na biza.

A makon nan a muke ciki ne Gwamnatin Tarayya ta ba da izinin kara wa’adin kammala rajistar lambar dan kasa ta NIN zuwa ranar 31 ga watan Oktoba, 2021.