Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire ta Yammacin Afirka WAEC, ta ce za ta sanya bukatar lambar katin dan kasa ta NIN ya zama tilas ga masu zana jarrabawar a bana.
Jami’in hukumar a Najeriya, Patrick Areghan ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Talata a Jihar Legas.
- Zulum ya shammaci wasu malaman Firamare da jarabawar ba-zata
- Wutar daji ta kashe soja 25 da wasu 22 a Algeria
A cewarsa, hukuncin hakan ya biyo bayan umarnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar da tabbatar da kowane dan Najeriya ya mallaki katin shaidar dan kasa ta NIN wato National Identity Number.
“Ina amfani da wannan dama don sanar da cewa yayin da muke ci gaba da inganta al’amura a kasar nan tamu Najeriya, NIN za ta zama babban abin da ake bukata domin yin rajistar jarabawa daga kan daliban da za su yi WAEC a shekara ta 2022.
“Ka’idar itace ‘Babu NIN, babu shiga jarabawa!’.
“Saboda wannan dalili duk masu son yin jarrabawar dole ne su yi rajista da Hukumar Bayar da Shaidar dan Kasa domin samun lambar NIN.
“Wannan ya yi daidai da tsarin Gwamnatin Tarayya kamar yadda Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ba da umarni.”
Partrick ya ce, tuni hukumar WAEC ta bukaci dalibai da su mika lambar dinsu ga hukumomin makarantun da za su zana jarrabawar a bana.
Hukumar ta ce daga shekarar 2022, sanya lambar NIN yayin rajistar jarrabawar zai zama wajibi ga kowane dalibi.