Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa da gangan ya ki ya ba da sakamakon jarabawarsa ta kammalan sakandare (WAEC) a kakar zaben 2015.
Tsohon kakakin Buhari, Femi Adesina ne ya bayyana haka a littafin da ya wallafa kan shugabancin Buhari da kalubalen da ke ciki mai suna ‘Working with Buhari: Reflections of Special Adviser, Media & Publicity (2015-2023)’.
A babi na biyar a littafin Adesina ya ruwaito Buhari a cewa, “Ina duba wani durowa sai na ga kwafin takardun karatuna a ciki, amma duk da haka na ki bayyana su, saboda masu surutu a kai su ci gaba.”
Rashin gabatar da sakamakon jarabawar WAEC din Buhari dai ya jawo ka-ce-na-ce a zaben, inda ’yan adawa suka yi kokarin amfani da rashin ainihin takardun karatun nasa a matsayin dalilin hana shi tsayawa takara.
- Mai Ciki Ta Haihu A Kofar Gida Saboda Yaki Bayan Dokar Hana Fita A Mangu
- Za a halasta wa jami’an diflomasiyya sayen barasa a Saudiyya
Gabanin zaben, Buhari ya bayyana cewa kwafin takardun nasa na hannun Rundunar Sojin Najeriya, wadda ita kuma daga bisani ta ce beraye sun cinye takardun.
Sai bayan hawansa mulki ne dai, a watan Nuwamban 2018 da Magatakardar WAEC da wasu manyan jami’an hukumar suka mika wa Buhari satifiket dinsa.
A lokacin da Buhari yake karabr satifiket dinsa, ya bayyana cewa “babu yadda za a yi in halarci kwalejin hafsoshin soji a kasar Indiya da kuma Burtaniya, alhali ba ni shaidar jarabawar WASC da na zana a 1961.”
Ya kara da cewa a lokacin da yake makaranta abu ne mai matukar wahala mutum ya iya magudi.
Ya bayyana wa taron cewa: “Sai da muka zana jarabawar shiga aikin soja, a lokacin da muka so shiga aikin soja tare da abokina, Janar Musa Yar’Adua, wanda tare da shi muka shekara tara makarantar firamare da sakandarem kwana.
“Jarabawar ta ƙunshi darussan Ingilishi, lissafi da kuma ilimin yau-da-kullum.”