Ado Ahmad Gidan Dabino, Shugaban Kamfanin Wallafe-Wallafe da Shirya Fina-Finai na Gidan Dabino International, fitaccen marubucin littattafan kirkirarrun labarai na Hausa ne kuma mai shirya fina-finan Hausa. Yana daya daga cikin ’yan kasa da aka ba lambar girmamawa ta kasa a shekarar 2014. Wane ne Ado, wane tudu da gangare ya hau har ya cimma wannan nasara kuma yaya ya ji a ransa da aka ambaci sunansa a matsayin wanda kasa ta karrama da lambar girma ta MON? Wadannan da wasu tambayoyi ke kunshe cikin wannan tattaunawa da wakilinmu ya yi da shi.
Mene ne tarihinka a takaice?
An haife ni a 1964 a garin Danbajima, da ke Karamar Hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano. Kuma na yi rayuwa a cikin birnin Kano, domin a Zangon Bare-Bari aka yaye ni. Nan na yi karatun allo kuma na yi karatun Islamiyya a ’Yanmota, makarantar Sheikh Malam Tijjani na ’Yanmota. Ban yi karatun zamani ba a lokacin da nake karami, sai da na kai shekara 20 a duniya sannan na shiga makarantar manya ta dare (Adult Ebening Classes) da ke Shahuci. Na shiga a 1984, na yi shekara biyu na kammala karatun firamare, domin kuwa idan dalibi ya zo, ana koya masa abin da ya wajaba ne, ba sai ka yi shekara shida ba kamar yadda yara ke yi. Iyaka fahimtarka, iya abin da za a koya maka. Bayan na gama, a 1986 na tafi Makarantar Ilimin Manya ta dare ta Kano. A can na yi shekara hudu na samu ilimin sakandare. Wato shekara biyu na yi karamar sakandare, shekara biyu kuma a babbar sakandare. Ka ga a shekara shida ke nan na yi karatun firamare da sakandare. Daga nan na ci gaba da harkar rubuce-rubuce, ban sake shiga harkar karatu ba sai ’yan kwasa-kwasai da na yi na shekara daya a fannin aikin kafinta, shekara daya kuma na fannin koyon ilimi na musamman, domin koyar da makafi. Daga nan kuma sai a shekarar 2005 na tafi Jami’ar Bayero, na yi Diflomar kwarewa a fannin watsa labarai. Wannan shi ne iyakar ilimina na zamani, sai kuwa ’yan kwasa-kwasai da na yi nan da can a harkar rubutu da harkar fim da sauransu.
Yaya aka yi ka samu kanka a cikin harkar rubuce-rubuce?
Tun sama da shekara 30 zan ce, ko kuma ma in ce tun ina yaro, ina tare da yayata, muna daukar wasan kwaikwayo a rikoda, ita ta yi muryar mace, ni kuma in yi muryar namiji, ta dauka a kaset. Daga nan na fara, sai kuma da na girma na ci gaba da rubuta ’yan kananan labarai.
A wace makaranta ke nan. Domin ka ce ba ka yi karatun zamani a yarintarka ba?
Ai abin da nake nufi a nan, ba wai rubuce-rubuce ba, amma murya. Za mu zauna ne mu rika kamar wasan kwaikwayo, muna daukar muryoyinmu a rikoda. Bayan kuma na girma, na kai shekara 20, kafin in shiga Makarantar Ilimin Manya ta Shahuci, ai na iya rubutu, domin na fara koyon karatu da rubutu wajen abokai. Saboda haka ina da dan abin da na dan fara, daga baya kuma na zo na shiga makarantar. Da na gama wannan karatu, sai na fara rubuta gajerun labarai ina aika wa Rediyo Dusche Welle. Akwai wani shiri da suke kira Taba Ka Lashe, suna karata gajerun labarai, suna biyan kudi, kamar Duchmark 100 zuwa 150. A 1986 zuwa 1987 na aika da labarai sama da guda goma. Daga nan ne ma aka ba ni shawarar cewa ya kamata in fadada wasu zuwa littafi. Tun ina firamare nake wannan rubutu kuma na zo na shiga sakandare. Lokacin da na gama sakandare ne na fara buga littafina na farko mai suna In Da So Da Kauna, yau shekara 29 ke nan.
Littafinka na In Da So Da Kauna, an ce soyayya ce tsakaninka da wata yarinya ta ja ka rubuta shi, ina gaskiyar wannan batu?
Gaskiyar magana, wannan haka ne. Lokacin da na yi littafin, akwai abin da rayuwata ce na fada, wani bangaren daga ciki amma na dan canja wasu bayanai saboda wasu dalilai. Amma gaskiya ne akwai abin da ya faru kuma na fadi wasu daga ciki, wasu kuma ban fada ba.
Ita wannan yarinya da ka kuka yi soyayya, ko ka aure ta?
Ban aure ta ba, ta dai auri wani kuma ta haifi ’ya’ya uku ko hudu, amma na mance adadin.
Daga wancan lokaci da ka rubuta In Da So Da Kauna, ko littattafai nawa ka rubuta?
Littattafaina goma sha, wadanda suka hada da In Da So Da Kauna (1 da 2), Hattara Dai Masoya (1 da 2), Wani Hani Ga Allah (1 da 2), Masoyan Zamani (1 da 2), Duniya Sai Sannu, Kaico, sai Mata Da Shaye-Shaye, Malam Zalimu. Sai wanda muka yi hada-ka ni da Sani Yusuf Ayagi, Tarihin Sarkin Ban Kano, Alhaji Mukhtar Adnan. Ka ga littattafai 13 ke nan wadanda aka buga.
Cikin wadannan littattafai, wanne ne za a kira shi da Bakandamiyarka?
Bakandamiyar littattafaina a wurin mutane, shi ne In Da So Da Kauna, domin shi suka fi so kuma shi suka fi sani, shi ya fi fito da ni a wurinsu kuma shi ne aka fi sayar da kwafinsa, an sayar da sama da kwafi 300, 000 amma kuma ni ba shi na fi so ba. Ni na fi son littafin Wani Hani Ga Allah.
Saboda me?
Saboda wancan, akwai yarinta tare da ni. A lokacin da na rubuta littafin In Da So Da Kauna, ba ni da mata, ba ni da da ko daya, wato ban ma yi aure ba a lokacin. Ka ga 1992 na yi aure, sai da na shekara biyu da sayar da littafina na daya da na biyu sannan na yi aure. Amma shi wannan, na yi aure, na haihu, saboda haka akwai hankali sosai, girma ya dan samu.
Sai ga shi Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta zabe ka a daya daga cikin ’yan Najeriya da ta karrama da lambar girmamawa ta MON, musamman saboda gamsuwa da hidima ga al’umma da kake yi, yaya ka ji da wannan bayani ya iske ka?
Da na ji wannan albishiri kuma a matsayina na farko, wato ni ne na farko a cikin marubuta rubutun adabi na zamani da ya samu lambar, na ji dadi kuma na dauka cewa nasara ce tamu gaba daya. Kuma ana sane da duk abin da kake yi da gudunmawa da hobbasa da kake yi a duk fannonin rayuwa. Tun daga shekara 28 ina ta fafutika a cikin wannan harka, ba don in samu kudi ba nake yi, sai don dai kawai ci gaban al’umma da sauransu. To kuma ga shi har Allah Ya so an fara saka maka daga abubuwan da kake yi. To na ji dadi kwarai da gaske. Kuma na gaya maka cewa wanda ya aika da sunana, har zuwa yau ban taba ganinsa da idona ba, wato wani mutum mai suna Sani Mafara, ma’aikaci ne, dan jarida ne a Jihar Zamfara. Har yau ban taba ganinsa ba, ko hotonsa ban taba gani ba, sai dai a intanet, sai dai a waya, wato mu yi magana a waya ko kuma I-mel, ko a Facebook ma ba mu magana da shi, sai a waya. Saboda haka, wani abu ne ya gani ya dace, ganin irin abubuwan da muke, ya aika da sunana.
A shekarar 2012 ya tuntube ni, ya shaida mini cewa ya kamata a aika sunana domin ganin an ba ni lambar yabo ta kasa. Na ce haba, ai ban kai nan ba, domin dai ni ba wani babban dan boko ba ne, ba wani babban ma’aikacin gwamnati ba. Shi ne ya ce ai ba nan take ba, domin irin hidimar da nake wa al’umma ta fannin rubuce-rubuce, fadakarwa da fina-finai da sauransu, su ma abin dubawa ne. Ya nemi in aika masa da tarihina, ni kuwa na rubuta shi shafuka da dama, na tura masa. Shekara biyu ke nan, ni har ma na mance, domin bara ban ga sunana ba, don haka ba ni da masaniyar ma za a ba ni lamba. Ina ofishin Farfesa Abdalla Uba Adamu, sai na ji kira, wani dalibi ne ma yake gaya mini. Ya ce na ga sunana a Premium Times, wai an ba ni lambar girmamawa ta kasa. Na ce ba ni ba ne. Ya rantse mini da cewa wallahi ni ne, na ce ‘a’a, mu je.
Wane tasiri kake ganin wannan lambar girmawa ta MON za ta yi a rayuwarka nan gaba?
Tasirinta shi ne na kafa tarihi, a matsayina na wanda yake ba mai dogon karatu ba ta fuskar ilimin zamani kuma ni ba mai kudi ba, ba mai kaza da kaza ba, aka ba ni wannan lamba. Za ta yi tasiri matuka, za ta kara mani kwarin gwiwa, ta kuma kara wa wadansu. Wadanda suke ganin cewa ba za su kai wani matsayi ba, yanzu za su gane cewa lallai za su iya kaiwa kowane matsayi a rayuwa, idan Allah Ya sa sun tsaya sun jajirce. Kuma wannan yana nuna cewa mutane suna ganin abin da kake yi kuma ana yabawa. Kuma wannan zai sanya maka ka rika yin hakuri da rayuwarka cewa duk abin da ka sa a gabanka kana hakuri kuma ka yi da gaske, ka yi shi don Allah, Allah zai taimake ka. Wadanda suke ganin cewa shirme kake yi, shashanci ko kaza da kaza, to yanzu duniya ta nuna ko Najeriya ta nuna maka cewa ba shashanci kake yi ba. Abin da kake yi din nan, wani zai dauke ka mahaukaci, wani zai dauke ka ba ka san darajar kanka ba ko ba ka da tattali. Wani zai dauke ka ko ba ka son kudi da sauransu. Dukan irin wadannan batutuwa babu irin wanda ba za ka ji ba, amma ni wannan ba zai hana ni yin abi da na sa gaba ba kuma na amince da shi.
Maganar iyali fa?
Ina ganin ’ya’yana za su yi alfahari, matata za ta yi alfahari da wannan, domin ni mahaifinsu na kai wani matsayi a kan aikina, wanda Najeriya ta yarda da ni, ta ga mutuncina, ta ga darajata da abin da nake yi. Wannan ko bayan raina, idan suka rubuta sunansu, wance Ado Ahmad Gidan Dabino (MON), za su ci gaba da rayuwa da wannan lambar, koda ba na raye, ita lambar tana raye, domin ta fi kudi wanda za ka kashe, ta fi wani abin hannu wanda za ka mallaka ya kare amma wannan lambar har iya rai da mutuwa, tana nan har abada kuma ba kowa ake samu a ba ba. Tunda in an duba Najeriyar gaba daya, za ka ga mutane nawa ne ake ba irin wannan lambar? Ta yiwu a unguwarku gaba daya ka ga babu mai ita sai kai, ka ga wannan abu ne na nasara da jin dadi a rayuwa.
Zuwa yanzu matanka nawa da kuma ’ya’ya?
Yanzu ina da mata daya da ’ya’ya biyar. Ina da Fatima, ita ce babba sai Ahmad sai A’isha, sai Adam sai kuma Hajara, ita ce ta biyar.
Ga marubuta masu tasowa, wace shawara ko jan hankali za ka yi musu domin su kai ga nasarar taka irin gwadaben da ka taka?
Shawarar da zan ba su ita ce, duk abin da za su yi, su yi shi da gaske. Duk abin da za su yi, su yi da gaskiya da amana. Duk abin da za su yi, su sa Allah a ciki. Duk abin da za su yi, su kula cewa me suke yi, yaya za su taimaka wa al’umma da shawara? Koda ba wai sai ka ba mutum kudi ba, a’a, shawara ma kanta wata aba ce kuma shawara ta gaske. Kuma idan za su yi rubutu, su kula da me suke rubutawa ga mutanensu, yadda al’ummarsu za su amfana. Koda harkar kungiyoyi za su yi ko fina-finai, nan ma ya kamata su yi koyi da abin da na baya suka yi, wadanda har suka samu wani abu na yabo, wanda duniya za ta kalle su. To idan suka yi wannan insha Allahu wata rana su za a ba irin wannan lambar karramawa ta kasa.