✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Lalong ya bude makarantun Filato

Jihar Filato za ta sake bude makarantu daga ranar 30 ga watan Oktoba bayan da suka shafe watanni a rufe sakamakon barkewar annobar COVID-19.  Gwamna…

Jihar Filato za ta sake bude makarantu daga ranar 30 ga watan Oktoba bayan da suka shafe watanni a rufe sakamakon barkewar annobar COVID-19. 

Gwamna Simon Lalong, ta bakin Kakakinsa, Dokta Makut Simon Macham, ya ce matakin na zuwa ne bayan wani taro da ya yi da dukkanin masu ruwa da tsaki na jihar a kan daukar matakan hana yaduwar cutar a dukkanin makarantun jihar.

Ya ce an horas da malamai da shugabannin makarantun jihar kan matakan hana yaduwar cutar.

Sanarwar ta ce daliban makarantun firamare ‘yan aji shida za su fara karatu daga ranar 19 zuwa 23 ga watan Oktoba, don shirye-shiryen jarrawar fita.

Tun a watan Maris ne dai aka rufa makarantu a dukkan sassan Najeriya da nufin hana coronavirus yaduwa.