Gwaman jihar Filato Simon Bako Lalong da iyalansa ba su kamu da cutar coronavirus ba, kamar yadda gwaji ya nuna.
Sakamakon gwajin, wanda Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC), ta yi wa iyalan gwamnan a dakin bincikenta da ke Abuja ne ya nuna hakan.
- COVID-19: ‘Gazawar’ Buhari wajen daukar mataki ta haifar da matsala
- Coronavirus: Gwamnatin Filato ta rufe iyakokin jihar
Da yake magana a kan wannan al’amari, Gwamna Lalong ya ce ya dauki wannan mataki na yin wannan gwaji tare da iyalansa ne, don zama abin misali a fafutukar da ake yi don ganin an hana yaduwar annobar.
‘’Wannan cuta ta coronavirus ba cuta ce da mutum zai ce don ya kamu da ita shi ke nan ya mutum ba.
“Idan ba mu natsu ba, za mu rika mutuwa saboda tsoro don mun kamu da wannan cuta.
“Don haka muna kira ga al’ummar jihar Filato su fito su yi gwajin wannan cuta, musamman wadanda suka ga alamunta tattare da su’’, inji Mista Lalong.
Sai dai kuma ba a ko’ina ne ake da cibiyoyin gwajin cutar ba, ko da yake hukumar NCDC ta ce ana kan aikin samar da dakin bincike a Jos, babban birnin jihar ta Filato.
Bugu da kari kuma ba kowa ake yiwa gwajin ba a halin da ake ciki sai wadanda suka yi mu’amala da wadanda aka tabbatar sun kamu, da wadanda suka nuna alamun kamuwa, da kuma wadanda suka dawo daga kasashen waje.
Da tsakar daren Alhamis ne dai dokar da gwamnatin jihar ta kafa ta hana fita sam ta fara aiki.