Shugaban Kasar Amurka Joe Biden, ya bukaci Gwamnan New York, Andrew Cuomo, ya yi murabus bayan bincike ya same da laifin lalata da mata 11.
Biden, a wani taron manema labarai a Fadar White House a ranar Talata, ya ce Gwamna Cuomo ba shi da wani zabi face ya yi murabus.
Da aka tambaye shi ko ya kamata a tsige gwamnan, Biden ya ce, “Ya kamata mu yi abin da ya dace. Murabus ya kamata ya yi.
“Na san cewa majalisar dokokin jihar na iya yanke hukuncin tsigewa, ban san me suke ciki ba, saboda ban gama karanta bayanan ba,” inji shugaban, wanda ya ce bai samu damar zama da Cuomo ba tukuna.
Babban Lauyan New York, Letitia James ya fitar da rahoto a ranar Talata, yana mai cewa, a wani taron manema labarai, “Gwamnan ya yi wa ma’aikatan jihar na yanzu da tsoffin ma’aikata fyade wanda kuma laifi ne karkashin dokokin tarayya da na jihohi.”
Binciken mai zaman kansa ya gano cewa Cuomo ya tursasa mata da yawa, yawanci ’yan mata, ta hanyar sumbata, runguma da kuma kalaman batsa.
A cikin wani bidiyo da yake mayar da martani, Cuomo ya ce shi bai yi wa kowa fyade ba kamar yadda ake zargi.
Ya bayyana kansa a matsayin jagora mai yaki da masu cin zarafin mata da fyade, yana mai neman afuwar Charlotte Bennett, daya daga cikin wadanda ke tuhumar sa, wadda a cewarsa yake kokarin taimaka wa.
Ya ce zai kafa sabbin manufofin kawo karshen cin zarafin mata a jihar.