Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta gabatar da tuhume-tuhume guda takwas a kan DCP Abba Kyari a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin hannunsa a fataucin hodar Iblis.
Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da Gwamnatin Tarayya ta amince ta mika fitaccen dan sanda Abba Kyari ga kasar Amurka don ya fuskanci hukunci kan badakalar sama da Dala miliyan daya.
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Watsi Da Dokar Ba Mata 35% na mukaman shugabanci
- Farashin man fetur ya yi tsadar da bai taba yi ba cikin shekara 10
NDLEA tana kuma zargin wasu ’yan sanda shida da suka yi aiki a karkashin DCP Kyari da hannu a badakalar ta Abba Kyari.
Sauran wadanda hukumar ta gabatar da tuhume-tuhumen kansu a gaban kotun su ne ACP Sunday Ogbuya da ACP Sunday James da Sifeta Simon Ariba da kuma Sifeta John Nuhu, wadanda duk suka yi aiki a Runduna ta Musamman kan Yaki da Miyagun Laifuka (IRT), wadda Kyari ya jagoranta kafin a dakatar da shi daga aiki.
Ragowar su ne Chibunna Patrcike da Emeka Alfphosus, wadanda aka kama su a filin jirgin sama na Enugu bisa zargin su da safarar miyagun kwayoyi ciki har da hodar Iblis.
Rahotanni sun bayyana cewa lauyoyin NDLEA karkashin jagorancin Mista Joseph Sunday, sun shigar da kara sun zargin Kyari da sauran ’yan sandan hudu da hada baki wajen safarar hodar Iblis mai nauyin fiye da kilogiram 17.
Hakan na zuwa ne bayan a safiyar Alhamis, Ofishin Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya fitar da sanarwar amincewa da bukatar Amurka na mika mata DCP Abba Kyari bisa zargin sa da alaka da fitaccen dan damfara Hushpuppi.
Hushpuppi wanda dan Najeriya ne mazaunin Hadaddiyar Daular Laraba, yana fuskantar shari’a a Amurka kan aikata damfara ta miliyoyin daloli.
Ana zargin Abba Kyari na da hannu wajen damfarar da Hushpuppi ya yi ta intanet da kuma tura haramtattun kudaden.
Da farko kotu ta sanya da 14 ga watan Fabrairun da ya gabata, a matsayin ranar da za ta yanke wa Hushpuppi hukunci, amma daga bisani ta dage zuwa watan Yuli.