✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LAFIYAR MATA DA YARA

Amsoshin tambayoyi Ko yara na samun tabin hankali? Ko yara na iya samun ciwon tabin hankali kamar yadda manya kan iya samu?   Amsa: Eh,…

Amsoshin tambayoyi

Ko yara na samun tabin hankali? Ko yara na iya samun ciwon tabin hankali kamar yadda manya kan iya samu?

 

Amsa: Eh, yara kan iya samun tabin hankali amma yawanci cututtukan da ke sa tabin hankali ga yara daban suke da irin wadanda suke sa tabin hankali ga manya. A manya idan an lura matsaloli irin su buguwa a ka da matsalar bacin rai da damuwa da shan kwaya su ne kan gaba wajen jawo ciwon tabin hankali.

A yara kuma yawanci matsaloli ne na tun suna ciki inda akan samu tangardar halittu na jiki ko kananan halittu, ko na wasu sinadarai. Misali, za a iya samun tangardar manyan halittun jiki (kamar a irin yaran nan masu karamin kai, ko masu babban kai sosai suna zuwa da alamu na tabin hankali) ko ta kananan kwayoyin halittun jiki na DNA, inda misalansu suka hada da ciwon nan na maloho wanda kari ne akan samu a halittun DNA. Shi wannan kari shi yakan sa ciwon. Akan ma iya samun tangardar sinadaran aikin jiki na yau da kullum. Irin wannan shi ya fi sa wa ’ya’yan Turawa matsalar tabin hankali.

A wasu lokuta kuma za a iya ganin yaran kamar suna da tabin hankali amma daga baya da girma ya zo sai a ga sun natsu. Misali, irin tsoron nan na yara da yakan yi yawa sosai ya zama kamar ma ciwo da dama da yara sun fara girma sun fara hankali yake tafiya.

Alamun matsalar a yara za a ga kusan daya ce da ta manya, domin ban da alamomin shi ciwon da ya yi sababin tabin hankalin, akwai alamun tabin hankali na yawan kebewa wuri guda, rashin fahimtar abubuwan da kan faru na yau da kullum da rashin koyon sababbin abubuwa, sai rashin girma yadda ya kamata, a wasu lokuta ma har da rashin kula ko rashin bambance abu mai hadari da marar hadari, ko ma yunkurin illata kai ko wasu sassan jiki.

Da zarar an ga irin wadannan alamu a yara yana da kyau a yi maza a shirya a kai su ga likitan yara, wanda zai duba shi ya tabbatar ko akwai matsala, ko kuma a’a kawai kuruciya ce (tunda ko masu iya magana kan ce kuruciya dangin hauka). Idan akwai matsala zai yi kokari ya nema wa yaron kulawar likitan kwakwalwa, inda da taimakon Allah da na magunguna ko ma tiyata idan ta kama (kamar ta zuke ruwan kai a masu matsalar katon kai) da na wasu sauran dabaru akan iya danne tasirin matsalar ga yaran.